Fadowar jirgi a Legas: Maimakon cetonsu, matasa sace kudi da wayoyin mutanen da hadari ya sama sukayi - Mai idon shaida

Fadowar jirgi a Legas: Maimakon cetonsu, matasa sace kudi da wayoyin mutanen da hadari ya sama sukayi - Mai idon shaida

Wani mazaunin titin Opebi a Legas, wanda ya shaida fadowar jirgi mai saukar angulu a unguwar ranar Juma'a ya bayyana rashin tausayin da ya gani tattare da mutan jihar Legas yau.

Ya nuna bacin ransa kan abinda matasan suka rika yi maimakon ceton rayukan wadanda hadarin ya rutsa da su.

Wani jirgi mai saukar Angulu, Bell 206, mai lamba 5N BQW, na kamfanin Quoron Aviation, ya fadi a cikin gari.

Jirgin ya taso daga garin Fatakwal, jihar Rivers ne dauke da fasinja daya da matuka biyu.

Wani mutum mai suna John, ya bayyanawa manema labaran Sahara Reporters cewa mutanen da suka fara isa wajen lokacin da jirgin ya fado kwashe kudade da wayoyin mutanen dake cikin jirgin sukayi.

Ya ce har da shi dake kokarin cetonsu an sace masa waya.

Yace: "Abin takaici ne muna wa kawunanmu irin haka, wasu mutane sun shiga wajen da gaggawa da sunan taimaka mana wajen fito da wadanda ke cikin jirgi ashe sace waya da kudadensu sukeyi."

"Har nima an sace min waya, na baiwa wani ne yayinda nike kokarin cetonsu amma wanda na baiwa ya gudu da ita."

Fadowar jirgi a Legas: Maimakon cetonsu, matasa sace kudi da wayoyin mutanen da hadari ya sama sukayi - Mai idon shaida
Fadowar jirgi a Legas
Source: Twitter

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng News

Tags:
Online view pixel