Aikin N6bn: Cacar baki ta barke a tsakanin tsohon gwamna Dankwambo da gwamna Yahaya

Aikin N6bn: Cacar baki ta barke a tsakanin tsohon gwamna Dankwambo da gwamna Yahaya

Wata rigimar siyasa na kokarin barkewa a tsakanin gwamnan jihar Gombe, Muhammad Inuwa Yahaya, da tsohon gwamna, Ibrahim Hassan Dankwambo, a kan wani aikin gina tashar mota a Gombe.

A ranar Talata ne gwamna Yahaya ya soki tsohon gwamna Dankwambo a kan yin watsi da aikin gina babbar tashar motoci wanda tsohon gwamnan ya bayar da kwangilar aikin a kan biliyan N6.2 tun zangon mulkinsa na farko a shekarar 2012.

Gwamna Yahaya ya yi zargin cewa akwai yaudara a cikin bayar da kwangilar aikin saboda tuni an kammala wani bangare na aikin duk da ba a ci koda kaso 43 na kammala aikin ba.

"Duk wanda ya kalli wannan aikin ya san akwai niyyar yaudara a cikinsa, har an yi fenti a wani bangare na aikin duk da ko tubalin fara gina wasu bangaren ba a saka ba.

"An bayar da kwangilar aikin ne a kan biliyan N6.2 tun a shekarar 2012, kuma ana saka ran cewa za a kammala aikin a cikin shekarar 2014, amma saboda rashin mayar da hankali irin na gwamnatin baya har yanzu ba a kammala aikin ba duk da an biya kusan biliyan uku daga cikin kudin kwangilar aikin," a cewar gwamna Yahaya.

Da ya ke mayar da martani a shafinsa na dandalin 'Facebook', Dankwambo ya bukaci gwamna Yahaya ya mayar da hankali a kan harkokin gwamnati sakamakon yada farfaganda da zargin gwamnatin baya.

Aikin N6bn: Cacar baki ta barke a tsakanin tsohon gwamna Dankwambo da gwamna Yahaya
Tsohon gwamna Dankwambo
Asali: Depositphotos

Jaridar Daily Trust ta wallafa cewa wannan shine karo na farko da tsohon gwamna Dankwambo ya taba mayar da martani a kan dumbin zargin almundahana da gwamnati mai ci tayi masa tun bayan shigarta ofis a ranar 29 ga watan Mayu na shekarar 2019.

DUBA WANNAN: Farfesa Wole Soyinka ya caccaki shugaba Buhari a kan shirin kirkirar wata sabuwar doka a Najeriya

Dankwambo ya ce ya kamata jam'iyyar APC ta daina fakewa da zargin gwamnatin baya saboda ta gaza cika alkawuran da ta daukarwa jama'a a matakin tarayya da jihohi.

A cewarsa, tun farko, gwamnatinsa ta kirkiri gina sabuwar tashar motar ne domin takaita yawaitar hare-haren da mayakan kungiyar Boko Haram ke kaiwa tashar motoci a jihar; "a loakcin ne muka ga cewar akwai bukatar mu samar da wata babbar tashar mota."

Dankwambo ya kara da cewa ya yi iya bakin koakrinsa lokacin da yake kan kujerar gwamnan jihar Gombe, yanzu kuma lokacin gwamna Yahaya ne, a saboda haka ya yi kokarin sauke alkawawuran da ya daukarwa jama'a.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel