NYSC ta fadi lokacin da zata bude sansanonin horas da matasa masu yiwa kasa hidima

NYSC ta fadi lokacin da zata bude sansanonin horas da matasa masu yiwa kasa hidima

- NYSC ta bayar da tabbacin bude sansanonin horas da matasan da zaran kwamitin PTF na COVID-19 ya bayar da umurnin hakan

- Don haka sai ta yi kira ga daliban da suka kosa su fara bautar kasar da su yi hakuri, su kuma jira, domin za su iya jin kira a kowanne lokaci

- Shugaban shirin NYSC ya ce cibiyar SAED ta taimaka wa rayuwar tsoffin matasan da suka samu horo a cikinta, da yawansu suna cin kashin kansu

Hukumar gudanarwar shirin matasa masu yi wa kasa hidima (NYSC) ta bayar da tabbacin bude sansanonin horas da matasan da zaran kwamitin PTF na COVID-19 ya bayar da umurnin hakan.

Hukumar ta ce da zaran kwamitin shugaban kasar ya bayar da umurni za a bude sansanonin, don haka dalibai su kwantar da hankulansu, tunda shiri ne da ya wajaba a kansu.

Shugaban shirin NYSC na kasa, Brg.Gen. Shuaibu Ibrahim ne ya bayar da tabbacin, yayin da kuma yake bayar da shawarar kawo shirin horas da yara tun daga matakin firamare da sakandire.

Shugaban NYSC din ya je jihar Gombe ne domin kai ziyarar gani da ido kan gyaran cibiyar koyar da sana'o'in dogaro da kai (SAED) ta shiyyar Arewa maso Gabas.

Ana gyaran cibiyar SAED ne bayan da iska mai karfi ta lalata ginin cibiyar, da ke a cikin sansanin horas da matasa na karamar hukumar Akko, da ke jihar.

KARANTA WANNAN: Buhari ya sallami Charles Dokubo, ya nada sabon shugaban shirin Jin-kai

NYSC ta fadi lokacin da zata bude sansanonin horas da matasa masu yiwa kasa hidima
NYSC ta fadi lokacin da zata bude sansanonin horas da matasa masu yiwa kasa hidima
Asali: UGC

Ya bayya cewa ba za a iya kwatanta muhimmancin horas da matasa sana'o'in dogaro da kai ba, don haka ya zama wajibi yaro ya fara koyon sana'a tun daga makarantun fimarare da sakandire.

Shuaibu Ibrahim ya kuma bayyana cewa cibiyar SAED ta taimaka wa rayuwar tsoffin matasan da suka samu horo a cikinta, inda da yawansu suka bude wuraren sana'a na kashin kansu.

Shugaban shirin ya kuma ce akwai kwamitin da aka kafa wanda ke sa ido ga tsoffin matasan shirin da suka ci gajiyar bashin CBN, bankin 'yan kasuwa, da gidauniyar NYSC, don tabbatar da cewa suna amfani da bashin kamar yadda suka dauki alkawari.

Dangane da batun bude sansanonin horas da matasa na shirin NYSC, ya ce hukumar gudanarwar shirin na ci gaba da tantance sansanonin don tabbatar da kyakkyawan muhalli.

Don haka sai ya yi kira ga daliban da suka kosa su fara bautar kasar da su yi hakuri, su kuma jira, domin za su iya jin kira a kowanne lokaci.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel