'Yan siyasa ne suke rura wutar rikicin Kudancin Kaduna - Dr A.B. Lamido ya caccaki 'yan siyasa

'Yan siyasa ne suke rura wutar rikicin Kudancin Kaduna - Dr A.B. Lamido ya caccaki 'yan siyasa

- Babban Fasto a Kaduna ya dora alhakin rikice-rikicen dake faruwa a yankin Kudancin Kaduna kan 'yan siyasa

- Yace sune suke tada hankalin al'umma ta hanyar hada rikicin addini dana kabilanci domin su cimma wasu bukatunsu

- Ya ce dole ne gwamnati ta sanya hannu a wannan lamarin domin samun tabbatar da zaman lafiya a yankin baki daya

Archbishop na jihar Kaduna kuma Bishop na Wusasa, Reverend Dr. A.B. Lamido, ya ce 'yan siyasa ne a Najeriya suke tada rikici na addini, kabilu da sauransu, inda ake ta zubar da jini saboda kawai su biya bukatunsu na siyasa. Sai dai kuma ya ce ya kamata a zauna a tattauna domin samar da zaman lafiya.

'Yan siyasa ne suke rura wutar rikicin Kudancin Kaduna - Dr A.B. Lamido ya caccaki 'yan siyasa
'Yan siyasa ne suke rura wutar rikicin Kudancin Kaduna - Dr A.B. Lamido ya caccaki 'yan siyasa
Source: Twitter

A cewar shi, zaman lafiya da cigaba yana da alaka da samun dangantaka mai karfi da wasu da kuma gina alaka marar yankewa a tsakani. Da alama dai yana magana ne akan rikicin Kudancin Kaduna, Lamido ya ce: "Taron sulhu tsakanin Fulani da mutanen Atyap da AVM Ishaya Aboi Shekari da Dr. Salim Musa Umar za su jagoranta a ranar 20 ga watan Agusta, 2020, babban mataki ne ga samar da zaman lafiya da sulhu a yankin Atyap.

"Taron wanda zai samu halartar shugabannin tsaro, da kuma jami'an kananan hukumomi, babbar hanya ce ta kawo zaman lafiya. Na duba abubuwan da za ayi magana a wajen taron, na tabbata idan har aka sanya su, Za suyi tasiri sosai wajen samar da zaman lafiya. Shugabannin al'umma, Malamai, da matasa dole ne su hada karfi da karfe wajen ganin hakan ya tabbata.

KU KARANTA: Da dumi-dumi: 'Yan Boko Haram sun kashe mutane 14 akan iyakar Najeriya da Kamaru

"Ya kamata a sanar da mutane yadda matsalar tashe-tashen hankula ya banbanta ta hanyar kabilanci da addini. Muna neman hanyar da zamu tattauna don habaka dangantakar zamantakewa da tattalin arziki domin inganta jin dadi da wadatar jama'a. Idan babu irin wadannan hanyoyi za a bukaci shugabannin al'umma su sauka daga mukamansu.

"Naji dadi sosai da irin wannan hanya da za a bi wajen dawo da zaman lafiya a Atyap. Hakan ya nuna cewa hanyar da al'umma suke bi wajen tabbatar da zaman lafiya da magance rikice-rikice na da alaka da yadda aka tsara samun zaman lafiya na tsawon lokaci. Ya kamata a shiga tsakani domin magance sake aukuwar rikice-rikicen.

'Muna kira ga gwamnatin jihar Kaduna da ta bayar da goyon baya ta kowacce hanya. Za a iya cimma hakan ta hanyar fadakarwa, samar da ababen more rayuwa a yankin domin rayuwar al'umma tayi inganci, sannan kuma hukunta duk wani wanda yayi kokarin tada zaune tsaye a yankin. Wannan labari ne na samun nasara, kuma muna fatan sauran wurare zasu yi koyi wannan hanya. Gaskiya ne cewa cigaba ba zai yiwu ba idan babu kwanciyar hankali."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel