Duk Bafulatanin da ya shigo jihar Benue a matsayin dan sakai sai mun aika shi gidan yari - Gwamna Ortom

Duk Bafulatanin da ya shigo jihar Benue a matsayin dan sakai sai mun aika shi gidan yari - Gwamna Ortom

- Gwamnan jihar Benue, Samuel Ortom ya bayyana cewa zai daure duk wani Bafulatani da ya kama ya shiga jihar a matsayin dan sakai

- Gwamnan ya bayyana hakane a yayin martani da yake mayarwa da kungiyar Miyetti Allah bayan ta sanar da cewa za ta kafa kungiyoyin sakai a fadin Najeriya

- Sai dai kuma kungiyar ta ce matukar gwamnan bai janye maganar ba za ta maka shi a gaban kotu

A ranar Alhamis ne gwamnan jihar Benue, Samuel Ortom, ya bayyana cewa zai yi amfani da karfin doka wajen tabbatar da ganin duk wani Bafulatani da ya shigo jihar a matsayin dan sakai ya tafi gidan yari.

Idan ba a manta ba, kungiyar Miyetti Allah, tayi hira da manema labarai a Abuja, inda ta bayyana cewa za ta fitar da 'yan kungiyar sa kai a duka jihohin kasar nan domin tabbatar da zaman lafiya.

Duk Bafulatanin da ya shigo jihar Benue a matsayin dan sakai sai mun aika shi gidan yari - Gwamna Ortom
Duk Bafulatanin da ya shigo jihar Benue a matsayin dan sakai sai mun aika shi gidan yari - Gwamna Ortom
Asali: Depositphotos

Da yake mayar da martani akan wannan magana, Ortom ta bakin sakataren shi na yada labarai, Terver Akase, ya gargadi Fulani da kada su sake su shiga jihar shi, ya ce kokarin da suke yi shine su kara karfin abubuwan da suke yi marasa kyau.

Haka ita ma kungiyar a lokacin da take martani akan wannan sanarwa ta gwamnan, ta yi barazanar kai gwamnan gaban kotu idan har bai janye maganar shi ba.

Sai dai kuma Ortom a lokacin da yake magana da manema labarai a ranar Alhamis, ya ce: "Babu wasu Fulani da suka isa su shiga jihar Benue matukar yana kan kujerar gwamna; ku kan ku kun san cewa karya suke baza su iya zuwa ba.

KU KARANTA: 'Yan sanda sun ceto wasu yara kanana guda 2 da aka garkame a cikin bandaki a Abuja

"Babu maganar kungiyar sakai ko daya a jihar nan kowacce iri ce. Dana same su sunce baza su yi amfani da kungiyar sakai ba a Najeriya. Wannan baza tayi aiki ba a nan.

"Muna da kungiyar mu ta sakai da take aiki a nan; muna da dokoki da masu kula da lafiyarmu da dabbobin mu.

"Saboda haka babu wani dan kungiyar sakai na Miyetti Allah da zai shigo jihar Benue yayi mana barazana. Mu mutanen Benue mun yarda da doka, saboda haka zamu kai su gidan yari."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel