Babban labari: FG ta fara shirin daukar tsofaffin ma'aikatan N-Power aiki

Babban labari: FG ta fara shirin daukar tsofaffin ma'aikatan N-Power aiki

- Gwamnatin tarayya ta bayyana cewa za a dauki ‘yan N-Power da aka yaye aiki a hukumomin gwamnati

- Hajiya Sadiya Farouq ce ta bayyana hakan a ranar Alhamis, 27 ga watan Agusta, a Abuja

- Sadiya ta ce ta umurci masu kula da Shirin Tallafa wa Matasa a Jihohi (NSIP) da su gabatar mata da jerin sunayen tsofaffin ‘yan N-Power din

Gwamnatin tarayya ta ce tana tattaunawa domin tabbatar da ganin cewa an dauki ‘yan shirin N-Power da aka yaye aikin gwamnati.

Jaridar Leadership ta ruwaito cewa ministar harkokin agaji da walwala, Hajiya Sadiya Umar Farouq a cikin wata sanarwa a ranar Alhamis, 27 ga watan Agusta, a Abuja ta hannun mai magana da yawunta, Nneka Anibeze, ta bukaci matasan da aka yaye da su kara haukuri kafin fitowar sakamakon kokarin da take yi.

Legit.ng ta tattaro cewa ta ce ta umurci masu kula da shirin tallafa wa matasa a jihohi (NSIP) da su gabatar mata da jerin sunayen tsofaffin ‘yan N-Power din da ke sha’awar shiga shirin.

Babban labari: FG ta fara shirin daukar tsofaffin ma'aikatan N-Power aiki
Babban labari: FG ta fara shirin daukar tsofaffin ma'aikatan N-Power aiki
Asali: Twitter

Ta ce: “An bayar da izinin biyan alawus din da rukunin farko da na biyu da suka kammala shirin suke bin bashi”.

“An riga a gabatar wa ofishin akanta janar na tarayya umarnin biyan alawus din watan Yuni, 2020 ga rukunin domin ya kara dubawa ya biya su.

“Abin da kawai ya rage a mika wa Ofishin shi ne na biyan alawus din rukuni na biyu na watan Yuli.”

KU KARANTA KUMA: An gudu ba a tsira ba: Masu kwalin karatun PhD na rige rigen neman aikin N20,000 a FG

Mun kuma ji cewa masu cin gajiyar shirin 14000 da aka cire sunayensu daga ofishin AGF a yayin biyan kudin watan Maris zuwa Yuni 2020, na daga cikin wadanda manhajar GIPMIS ta ki karbar bayanan bankunan biyan kudinsu.

A cewar rahoton ofishin AGF, duk wani mai cin gajiyar shirin da ke karbar albashi daga gwamnati ba zai samu kudinsa ba.

Ma'aikatar FMHADMSD ta bukaci wadanda abun ya shada da su gabatar da dalilan da ya sanya basu samu kudinsu ba daga ofishin AGF, inda ta sha alwashin yin mai yiyuwa wajen biyansu.

Idan har kuwa basu samu kudadensu ba saboda wani kuskure na daban, to ma'aikatar ta bada tabbacin biyansu cikin karamin lokaci da zaran ofishin AGF ya gyara kuskuren.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel