Yanzu Yanzu: FG ta dage dawo da zirga-zirgar jiragen waje zuwa 5 ga watan Satumba

Yanzu Yanzu: FG ta dage dawo da zirga-zirgar jiragen waje zuwa 5 ga watan Satumba

- Gwamnatin tarayya ta sake dage ranar dawo da zirga-zirgan jiragen waje zuwa ranar 5 ga watan Satumba

- Ma’aikatar sufurin jirage ce ta sanar da hakan a ranar Alhamis, 27 ga watan Agusta, a lokacin taron kwamitin fadar Shugaban kasa kan COVID-19, a Abuja

- Ta bai wa al'umman Najeriya hakuri a kan wannan sauyi da aka sake samu

- A baya dai gwamnatin tarayyar ta tsayar da ranar 29 ga watan Agusta don dawo da jigilar jiragen kasashen waje

Gwamnatin tarayya ta dage ranar dawo da zirga-zirgan jiragen waje wanda aka shirya yi a ranar Alhamis, 27 ga watan Agusta zuwa ranar 5 ga watan Satumba.

Legit.ng ta rahoto cewa ma’aikatar sufurin jirage ce ta sanar da hakan a ranar Alhamis, 27 ga watan Agusta, a lokacin taron kwamitin fadar Shugaban kasa kan COVID-19, a Abuja, babbar birnin tarayyar kasar.

Ma’aikatar ta sanar da ci gaban ne a shafinta na twitter, @fmaviationg, inda ta ba ‘yan Najeriya hakuri a kan dagewar da ta yi.

“Da dumi-dumi: Muna danasanin sanar da cewar an dage dawo da zirga-zirgan jiragen sama da aka shirya yi a ranar 29 ga watan Agusta zuwa ranar 5 ga watan Satumba 2020,” in ji ma’aikatar.

KU KARANTA KUMA: An gudu ba a tsira ba: Masu kwalin karatun PhD na rige rigen neman aikin N20,000 a FG

A wani labari na daban, mun kawo maku a baya cewa a ranar Juma’a, 24 ga watan Yulin 2020, filayen tashi da saukar jiragen sama 14 gwamnatin tarayya ta amince da su koma aiki.

Sannan a ranar 8 ga watan Yulin 2020 ne gwamnatin tarayyar ta bude filayen sauka da tashin jiragen sama na Legas da Abuja.

Har ila yau a ranar 11 ga watan Yuli aka bude filayen jiragen sama hudu da suka hada da na Fatakwal da ke jihar Ribas, filin sauka da tashin jiragen sama na mallam Aminu Kano, Maiduguri da kuma Owerri.

Kungiya daga hukuma kula da kamfanonin jiragen sama masu zaman kansu, sun dudduba filayen sauka da tashin jiragen saman kafin budesu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel