Soji sun gano masana'antar hada bama-bamai a Nasarawa, an damke mutum 410
Hukumar Sojin Najeriya a ranar Laraba ta ce daruruwan mambobin sabuwar kungiyar yan ta'adda, Darul Salam da ta fara tsirowa a jihar Nasarawa sun mika wuya.
Hakazalika jami'an Soji sun gano masana'antar kera bama-bamansu kuma sun ragargaza.
Hakan na kunshe cikin jawabin da kakakin hukumar Soji, Manjo Janar John Enenche, ya saki.
Eneche yace sun mika wuya ne bayan hare-haren da dakarun atisayen Operation Whirl Stroke suka kai tare da hadin kan jami'an wasu hukumomin tsari a garin Uttu, karamar hukumar Toto a jihar Nasarawa.
Daga cikin yan ta'addan akwai mata da yara.
Kakakin Sojin ya ce a ranar 25 ga Agusta, 2020, akalla yan ta'addan 410, suka mika wuya.
Bayan haka, jami'an Sojin Operation Whirl Stroke sun dira masana'antar kera bama-bamansu kuma aka gano makamai da rokoki da dama.

Asali: Facebook
A cewar jawabin: "Bayan hakan, Dakarun Operation WHIRL STROKE yayinda suke sintiri a Uttu, a ranar 26 ga Agusta 2020 sun dira masana'antar kera bama-baman kungiyar yan ta'addan Darul Salam."
"Yayin farmakin, Sojoji sun gano kayayyakin hada bama-bamai a wajen wanda ya hada da na'urar harba roka 6, buhun taki daya, buhun garin bindiga daya, gurnet 10, RPG daya, bama-mamai 2, rokoki 13 dss.
"Sai muka yi raga-raga da masana'antar yayinda Sojoji suka cigaba da binciken cikin daji domin kama sauran yan ta'addan dake kokarin guduwa." Enenche yace.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng