Zulum, shugaba nagari mai bautawa mabiyansa - APC

Zulum, shugaba nagari mai bautawa mabiyansa - APC

- Jam'iyyar APC ta kwatanta gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Zulum da daya daga cikin gwamnoni da ke bautawa jama'arsa

- Matamakin shugaban jam'iyyar APC, Yekini Nabena, ya sanar da hakan a cikin sakon taya gwamnan cika shekaru 51 a duniya

- Ya yi fatan lafiya da hikima masu daurewa ga gwamnan domin ci gaban jiharsa, jam'iyyar da kasar Najeriya baki daya

Jam'iyyar APC mai mulki, ta ce gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum na daya daga cikin shugabanni nagari masu bautawa jama'arsu.

Jam'iyyar ta sanar da hakan ne yayin da take taya Gwamnan murnar cikarsa shekaru 51 a duniya, jaridar The Nation ta wallafa.

A sakon taya murnar wanda mataimakin shugaban jam'iyyar APC, Yekini Nabena, ya fitar a garin Abuja a ranar Laraba, jam'iyyar ta ce: "Jam'iyyar APC, makusantanta da jama'ar jihar Borno suna taya shugaba nagari mai bautawa jama'arsa murnar zagayowar ranar haihuwarsa.

"Gwamnatin Zulum ta tabbatar da amfani da damarta wurin kammala ayyuka da yawa na more rayuwar jama'a wanda ta fara da kuma wanda gwamnatin da ta gabata ta fara.

"Babu shakka jama'ar jihar Borno sun yi sa'a.

"A yayin tuna yadda Gwamna Zulum ya saka wa Obiagelli Mazi, wata jajirtacciyar malamar makaranta, da kudi tare da karin girma, za a gane cewa gwamnan jajirtacce ne kuma yana son masu jajircewa.

"Akwai sauye-sauye da aka samu a fannin ma'aikatan gwamnatin jihar wanda ya sha banban da na baya.

Zulum, shugaba nagari mai bautawa mabiyansa - APC
Zulum, shugaba nagari mai bautawa mabiyansa - APC. Hoto daga Channels TV
Asali: UGC

KU KARANTA: Sarkin Kano, Aminu Ado-Bayero, zai kai ziyara masarautar Ilorin a ranar Alhamis

“Babu shakka Borno na cike da kalubale na tsaro, wanda ya taka rawar gani wurin durkusar da jama'ar jihar ta fannin zamantakewa da tattalin arziki.

"Amma abun jinjina shine yadda Gwamna Zulum ya dage wurin farfado da tattalin arzikin jihar ta hanyar kafa shirin mayar da manoma gona, tare da karfafa wa masu kananan kasuwanci guiwa.

“Jam'iyyarmu a matsayin masu goyon bayan sabbin tsare-tsare da shirye-shiryen Gwamna Zulum, za ta ci gaba da bashi goyon baya don tabbatar da ci gaban jihar.

"Muna masa fatan lafiya da hikima masu dorewa, wadanda zai yi amfani da su wajen tabbatar da ci gaban jihar, bada gudumawa wurin daukakar jam'iyya da kuma ci gaban kasa baki daya."

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel