Messi ba zai iya barin Barcelona ba sai ya biya £628m - Tsohon Dirakta a kungiyar

Messi ba zai iya barin Barcelona ba sai ya biya £628m - Tsohon Dirakta a kungiyar

-Shirin da Lionel Messi ke yi na barin Barcelona na tayar da rikici a cikin kungiyar kwallon

- Shahrarren dan kwallon ya bayyanawa shugabannin kungiyar cewa yana son barinsu

- Dan takaran kujeran shugabancin kasar kungiyar Barelona kuma tsohon Dirakta ya ce wajibi ne Messi biya wasu makudan kudi inda yana son tafiya

An bayyanawa Lionel Messi cewa bai da girmama manya kuma abu daya da zai sa ya bar Barcelona yanzu shine idan ya biya kungiyar £628million, Mirror ya ruwaito.

Masoyan Barcelona sun rikida bayan Messi ya bayyana niyyar fita daga kungiyar kwallon bayan shekaru 20 yana taka musu leda.

Dan takaran kujeran shugabancin kungiyar Barcelona kuma tsohon Dirakta, Toni Freixa, ya ce Messi ba kyauta ba kuma saboda haka wajibi ne ya biya kungiyar £628million kafin ya iya tafiya.

"Ni ko a jikin na Messi ya tafi saboda komai na da karshe. Abinda takaicin shine ya yi hakan ta wani hanya mara da'a kuma ba tare da mutunci ba."

"Sai ya cika kwantaraginsa kuma wajibi ne Messi ya kawo €700m (£628m) kafin ya tafi." Ya bayyana.

Messi ba zai ya barin Barcelona ba sai ya biya £628m - Tsohon Dirakta a kungiyar
Messi ba zai ya barin Barcelona ba sai ya biya £628m - Tsohon Dirakta a kungiyar
Asali: UGC

A bangare guda, Shahararren ‘dan kwallon Duniya, Lionel Messi ya ya ki fitowa aiki a yau Ranar Laraba.

Dan wasan ya sanar da kungiyarsa ta Barcelona cewa ba zai fito aiki a yau Ranar Laraba ba.

Sabon darektan wasannin da kungiyar Barcelona ta nada, Ramon Planes ya bayyana matsayar ‘dan wasan a ranar 26 ga watan Agusta, 2020.

Ramon Planes ya ke cewa “Messi ya fada mana ba zai fito wasa ba.”

Planes ya yi wannan bayani ne a lokacin da ya ke kaddamar da sabon ‘dan wasan gaban da Barcelona ta saya, Joao Trincao.

“Duk wata tattaunawa da za ayi za ta zama tsakanin bangarori biyu (kungiyar da ‘dan wasan), Saboda girmamawa, ba za mu bayyana tattaunawarmu ba.”

KU KARANTA: Muna zagaye na biyu ya mutu: Cewar Karuwar da wani mutumi ya mutu tare da ita

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel