Tashin hankali: Matar aure ta kama mijinta dumu-dumu yana lalata da mahaifiyarshi

Tashin hankali: Matar aure ta kama mijinta dumu-dumu yana lalata da mahaifiyarshi

- Wani abin kunya da rashin dadin ji da ya faru akan uwa da danta ya sanya kotu na shirin yanke musu hukunci shekara 20 a gidan yari

- Matar wani mutumi ta kama shi dumu-dumu yana lalata da mahaifiyar da ta tsugunna ta haife shi

- Hakan ya sanya ta sanar da 'yar uwarta, inda ita kuma ta sanar da 'yan sanda halin da ake ciki

Matar aure ta kama mijinta kiri-kiri yana lalata da mahaifiyarshi, inda ake tunanin kotu za ta yanke musu hukuncin shekara 20 a gidan yari saboda wannan mummunan abu da suka yi.

Tony L Lavoie, daga Fitchburg,Massachusetts, an kama shi dumu-dumu yana lalata da mahaifiyarshi mai suna Cheryl Lavoie, mai shekaru 64, a watan Mayun wannan shekarar da muke ciki.

Tashin hankali: Matar aure ta kama mijinta dumu-dumu yana lalata da mahaifiyarshi
Tashin hankali: Matar aure ta kama mijinta dumu-dumu yana lalata da mahaifiyarshi
Asali: Facebook

Bayan an kira 'yan sanda domin bada rahoto kan lamarin, dan sanda ya fara haduwa da 'yar uwar matar Tony.

'Yar uwar matar ta bayyanawa dan sandan cewa, matar Tony ta kira ta a waya ta sanar da ita yadda ta iske mijinta yana lalata da mahaifiyarsa kafin ta kira 'yan sandan, kamar dai yadda Sentinel & Enterprise ta ruwaito.

Daga baya dan sandan yayi magana da uwa da dan domin jin ta bakinsu game da wannan lamari.

Su biyun duka sun bayyana cewa wannan shine karo na farko da suka fara, kamar yadda rahoton ya nuna.

KU KARANTA: An gurfanar da wata budurwa a gaban kotu kan tayi shigan banza da ta nuna tsiraicinta

Dan sandan ya ce Tony ya ce masa: 'Ni ma ban sani ba, kawai lamarin ya faru ne."

Daga baya Tony ya bayyanawa dan sandan cewa yana son a dauki mataki akan hakan, cewar dan sandan.

Bayan ya tambayi Cheryl, ita ma amsarta kusan iri daya ce da ta Tony, inda ta ce wannan shine karo na farko da suka fara, kuma ya samo asali bayan sun fara sumbatar juna.

Bayan yayi magana da duka wadanda ke da hannu a lamarin, dan sandan ya bayyana cewa ya samu isasshiyar shaida akan uwa da dan.

An gayyace su akan su bayyana gaban kotu ranar 20 ga watan Agusta.

Bayan bayyanarsu a kotu an bukaci su nesanta da juna.

Za su dawo kotun a ranar 27 ga watan Oktoba domin cigaba da shari'a.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng