Kaso 40 na maza ma su aure suna neman maza 'yan uwansu - Jaruma Halima Abubakar
A kwanakin baya ne jarumar fina-finan kudancin Najeriya (Nollywood), Halima Abubakar, ta wallafa wani sako mai sarkakiya a dandalin sada zumunta.
Bayan ta wallafa sakon, masu bibiyar shafinta a dandalin sada zumunta sun rokoi jarumar ta fassara kalamanta domin su fahimci ma'anar da ke cikinsa.
Jarumar ta wallafa cewa; "kar ku yi saurin zargin mutanen da ke yawan neman mata. Wasu daga cikinsu maza suke bukata ba mata ba. Kar ka illata kan ka. Ka karkade kurar jikinka ka kra gaba."
A yayin tattanawarta da jaridar Punch a kan ma'anar sakon da ta wallafa, jaruma Halima, 'yar asalin jihar Kogi ta bayyana cewa kaso 40% na maza ma su aure a Najeriya suna neman maza a boye.
"Muna da fiye da kaso 40% na maza ma su aure a Najeriya da ke neman maza, ko kana son yarda, ko ba zaka yarda ba, wannan magana haka take.
"Babban abin haushin shine; hatta iyalinsu basu san da hakan ba, sun boye mu su, suna jin tsoron bayyana musu.
"Haka suke sakawa matansu irin cututtukan da suka kwaso. Ni a nawa ganin zaifi kyau su fito fili, su fadi gaskiyar halinsu, su saka bukatunsu a gaba fiye da komai.
"Na san maza ma su aure da yawa da ke neman maza da mata. Ina fadar hakan ne saboda gaskiyane, masu irin halin ne suke korafi a kan maganata. Me yasa namiji zai ta sauya mace haka kawai, ya nemi wannan, ya nemi waccan, me ya ke nema idan ba namiji ba?.
"Mafi yawan 'yan Najeriya munafikai ne, basa son karbar gaskiya. Ni, Halima Abubakar, na fada cewa akwai maza ma su aure da ke neman maza da mata. Su taimaki rayuwar na gaba ta hanyar bayyana halinsu, idan kuma ba zasu iya ba, su hakura da aure kawai," a cewar jarumar.
DUBA WANNAN: Kotu ta dakatar da manyan motocin zuwa kudu daga aiki a jihar Kano
Sannan ta cigaba da cewa, "idan kuma haihuwa suke bukata kawai, zasu iya daukan raino. Abin haushi, wasu daga cikinsu ma suna da yara da yawa amma duk da haka suke neman maza.
"Na dade ina ankarar da jama'a hakan, yanzu ne lokacin da zan yi magana irin wannan ya zo."
Jarumar ta yi watsi da ma su zargin cewa ta na yiwa tsohuwar kawarta, Tonto Dikeh, shagube ne kamar yadda wasu kafafen yada labarai ke yadawa.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng