Ban taba karbar cin hanci ba tunda na fara aikin dan sanda - Cewar Akua Gaddafi jami'ar 'yar sanda

Ban taba karbar cin hanci ba tunda na fara aikin dan sanda - Cewar Akua Gaddafi jami'ar 'yar sanda

- Mace ta farko a cikin jami'an 'yan sandan kasar Ghana wacce ta zagaye kasashe hudu na yankin Afrika ta Yamma akan babur, Akua Gaddafi ta bayyana cewa tunda take bata taba karbar cin hanci ba

- A cewar Akua, labarin cewa 'yan sanda na karbar cin hanci duka karyane domin kuwa ita bata taba ganin wani yayi ba da idonta

- Budurwar dai na aiki a bangaren binciken manyan laifuka na hukumar 'yan sandan kasar Ghana

Akua Gaddafi, mace ta farko a cikin jami'an 'yan sandan kasar Ghana da ta zagaye kasashe hudu na yankin Afrika ta Yamma a cikin kwana daya ta bayyana cewa tunda take bata taba karbar cin hanci ba.

Jami'ar mai kokari a wajen aikinta, kamar yadda mordernghana.com ta ruwaito, ta bayyana hakane a wata hira da tayi da Ato Kwamina da kuma Frema Adunyame a gidan talabijin na Citi TV.

Ban taba karbar cin hanci ba tunda na fara aikin dan sanda - Cewar Akua Gaddafi jami'ar 'yar sanda
Ban taba karbar cin hanci ba tunda na fara aikin dan sanda - Cewar Akua Gaddafi jami'ar 'yar sanda
Asali: Facebook

Da aka tambayeta ko ta taba yin irin wannan harkar, ta ce: 'Ban taba ba, shin mai yasa ma zan karba; saboda wani dalili? Menene dalilin da zai saka na karbi wannan cin hancin da kuke magana a kai?'

KU KARANTA: Hotuna: Kamfanin mota na Najeriya ya gwangwaje hukumar 'yan sanda da motoci masu dan karen kyau

Bayan haka Akua ta kara da cewa bata taba ganin wani jami'in dan sanda a kasar Ghana da ya karbi cin hanci ba, saboda haka ta bayyana cewa hakan duka jita-jita ce ake cewa jami'an suna karbar cin hanci.

"Ina yawan jin wannan jita-jitar tana yawo, amma ban tunanin gaskiya ce, saboda ban taba gani ba tunda nake; dan sanda ya karbi cin hanci, ban taba gani ba a rayuwata," ta ce.

Akua dai a yanzu tana aiki a bangaren binciken manyan laifuka na hukumar 'yan sandan kasar Ghana.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel