Ba zan taba daura auren da angon bai taba ganin amaryar babu kwalliya ba - Fasto Migwi

Ba zan taba daura auren da angon bai taba ganin amaryar babu kwalliya ba - Fasto Migwi

- Babban faston kasar Kenya, Godfrey Migwi, ya sanar da mabiyansa cewa ba zai sake daura aure ba matukar angon bai taba ganin amaryar babu kwalliya ba

- Ya bayyana cewa, yawan canza halittar fuska da amare ke yi ne yake kawo matsalar mutuwar aure da ta zama ruwan dare

- Faston yayi kira ga sauran fastoci 'yan uwansa da su guji daura aure ba tare da angon ya ga fuskar amaryar ba na tsawon makonni uku

Babban faston kasar Kenya, Fasto Godfrey Migwi, ya sanar da cewa ba zai sake daura aure ba matukar angon bai taba ganin amaryar ba babu kwalliya.

Faston ya ce dole ne ango ya ga fuskar amaryarsa ba tare da kwalliya ba na a kalla makonni uku kafin auren.

Ya kara da cewa, wannan ne babban dalilin da yasa aure ke mutuwa a wannan zamanin, shafin Linda Ikeji ya wallafa.

Migwi ya yi kira ga sauran masu coci da su bi ayarinsa domin rage yawaitar mutuwar aure da ya zama ruwan dare yanzu.

Ya wallafa cewa, "Na yanke shawara a matsayin na babban fasto kuma masanin Ubangiji cewa, da tsarkin mulkinsa da kuma baiwar da yayi wa mutanensa, ba zan sake daura aure ba a cocina matukar angon bai taba ganin amaryar na tsawon sati uku ba babu kwalliya."

KU KARANTA: Yadda mijin mahaifiyata ya kwashe shekaru yana lalata da ni - Fatima Ada

Ba zan taba daura auren da angon bai taba ganin amaryar babu kwalliya ba - Fasto Migwi
Ba zan taba daura auren da angon bai taba ganin amaryar babu kwalliya ba - Fasto Migwi. Hoto daga shafin Linda Ikeji
Asali: Twitter

A wani labari na daban, wani matukin motar haya mai shekaru 43 mai suna Idris Azeez, ya sanar da wata kotun gargajiya da ke Ile-Tuntun a Ibadan jihar Oyo, cewa matarsa mai suna Morenikeji ta bayyana masa kwartonta a matsayin babban yayanta.

Morenikeji ta kai korafi gaban kotun inda take bukatar a raba aurensu saboda Azeez ba shi da kula a matsayinsa na mijinta, kuma yana dukanta ba tare da dalili ba.

Ta bada labarin yadda ta taba karbar bashin banki domin fara sana'a amma Azeez ya handame tare da yin watanda da shi. Amma a yayin martani, Azeez ya ce Morenikeji na sane da cewa yana fuskantar wasu kalubale.

Ya ce, "Ta san cewa ni direba ne kuma motata ta lalace kafin mu yi aure. Hakan ne yasa na gaza kula da 'ya'yanmu. A lokacin da na samu mahaifiyarta don sanar mata da yadda take kyautar rashin hankali, mahaifiyarta ta ce kada in sake kawo karar diyarta saboda bata sanni ba.

"Ta kara da cewa a matsayin bazawara na ganta na aura, toh idan lokacin da za ta tafi wurin wani mijin yayi, in bar ta."

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng

Tags: