Sarkin Kano, Aminu Ado-Bayero, zai kai ziyara masarautar Ilorin a ranar Alhamis

Sarkin Kano, Aminu Ado-Bayero, zai kai ziyara masarautar Ilorin a ranar Alhamis

Sarkin Kano, Alhaji Aminu ado Bayero, zai ziyarci tsohuwar birnin Ilorin mai tarin tarihi a ranar Alhamis, 27 ga watan Augustan 2020, jaridar Solacebase ta wallafa.

Hakan yana daga cikin zagayen rangadi da yake yi a masarautun da ke fadin kasar nan, tun bayan hawan shi karagar sarautar Dabo a watan Maris na wannan shekarar.

Kamar yadda takardar da mai bai wa Sarkin Ilorin shawara na musamman a harkar yada labarai, Mallam Abdulazeez Arowona ya fitar a ranar Litinin, ya tabbatar da wannan ci gaban.

Takardar ta ce, "Nan da ranar Alhamis, 27 ga watan Augustan 2020, Mai martaba, Sarki Ilorin, Alhaji Dr. Ibrahim Sulu Gambari, zai karba bakuncin Mai Martaba Alhaji Aminu Ado Bayero, sarkin Kano.

"Idan ya iso filin sauka da tashin jiragen sama na Ilorin, manyan masu sarauta na masarautar Ilorin za su karbesa da kilisa inda za su shiga da shi cikin birnin."

"Bakon Sarkin zai shiga sallar Juma'a da kuma addu'a ta musamman da aka shirya don girmama shi tare da fatan nasarar mulkinsa, wanda za a yi a ranar Juma'a, 28 ga watan Augustan 2020," takardar tace.

Sarkin Kano, Aminu Ado-Bayero, zai kai ziyara masarautar Ilorin a ranar Alhamis
Sarkin Kano, Aminu Ado-Bayero, zai kai ziyara masarautar Ilorin a ranar Alhamis. Hoto daga Solacebase
Asali: Twitter

KU KARANTA: Zargin neman mata: Matar aure ta wanke mijinta da acid, alkali ya daureta

Takardar ta ce ziyarar tamkar ganin gida ce ga basaraken, domin kuwa jika ne ga sarkin Ilorin na takwas, Shehu AbdulKadir Dan Bawa, kuma dan uwa ga sarkin yanzu, Alhaji Ibrhaim Sulu-Gambari.

Hakazalika, takardar ta yi kira ga mazauna jihar Ilorin da su nuna tsananin kishin kai kafin, yayin da kuma bayan ziyarar basaraken, ta hanyar kiyaye dokokin dakile annobar korona wacce NCDC ta fitar.

A yayin godiya ga jama'a a kan zaton haidin kansu da ake yi a yayin ziyarar, takardar ta yi kira ga jami'an tsaro da su kasance a shirye.

A wani labari na daban, Gwamnan jihar Zamfara, Bello Matawalle, ya yi kira ga sarkin Kano, Aminu Ado-Bayero, da ya yi amfani da kujerarsa wurin assasa hadin kai na yankin arewacin kasar nan.

Gwamnan ya yi wannan kiran ne ga sarkin yayin da ya kai ziyara gidan gwamnatin jihar a ranar sati, kamar yadda yake kunshe a wata takarda da mai bada shawara na musamman a kan fannin yada labarai ga gwamnan, Zailani Bappa, ya fitar.

Matawalle ya jaddada cewa arewa na matukar bukatar shugabanni da za su hada kan jama'a don komawa saiti daya na siyasa da al'adu.

"Mai martaba, arewa na bukatar shugabanninsu da za su hada kan jama'arta a siyasance da al'adance kamar baya," Matawalle ya ce.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel