NDLEA ta kama katon 607 na tramadol a Legas

NDLEA ta kama katon 607 na tramadol a Legas

Hukumar Yaki da Fatauci da Miyagun Kwayoyi ta Najeriya, NDLEA, ta kama katon 607 makare da kwayoyin tramadol guda 11,785,800 a Legas.

Kakakin hukumar NDLEA, Mr Jonah Achema a ranar Laraba 26 ga watan Agusta ne ya bayyana hakan, kuma ya ce shugaban hukumar Muhammad Abdallah ya ce jami'an kwastam sun taimaka wurin kamen.

NDLEA ta kama katon 607 na tramadol
NDLEA ta kama katon 607 na tramadol. Hoto daga LIB
Asali: Twitter

Abdullah ya ce;

"An gano wannan ne a cikin wata kwantena mai lamba TCNU 9465832 mallakar wanda ake zargi da laifi da yan sanda suka mika wa hukumar NDLEA.

DUBA WANNAN: Yanzu-yanzu: Messi ya ce zai bar Barcelona

"Kawo yanzu an gano kwantena 3 da ake yi amfani da su aka boye haramtacciyar kwayar tramadol da wasu kwayoyin da aka shigo da su Najeriya daga kasashen waje."

Shugaban na NDLEA ya kuma ce yawan kwayoyin da aka kama da ke zuwa daga kasashen Pakistan a Asia – Hamburg a Nahiyar Turai – Nigeria lamari ne da masu safarar suka tsara don kaucewa hukuma.

A wani labarin daban, Legit.ng Hausa ta walllafa cewa NDLEA ta gano wani kwantena mai tsawon sahu arba'in shake da kwayar Tramadol da wasu haramtattun magunguna a tashar Brawal da ke Legas.

Mai magana da yawun hukumar Mr Jonah Achema ne ya sanar da hakan a ranar Laraba a birnin tarayya Abuja kamar yadda The Nation ta ruwaito.

A cewar sanarwar, Shugaban NDLEA, Muhammad Abdullah ya ce an gano wannan bayan da yan sanda suka kama wata kwantena mai tsawon kamu arbain shake da buroshi da katon din Tramadol 40 da wasu haramtattun kwayoyin.

"Idan za ku iya tunawa yan sandan Apapa a Legas sun kama wata kwantena mai tsawon kafa 40 shake da kwayoyi da ake zargin Tramadol ne da Kodin a ranar 6 a watan Agusta.

"An kama wannan kwantenar ne a ruwa sannan aka dauke ta aka kai tashar Apapa.

"Binciken da NDLEA ta gudanar ya yi sanadin gano wani kwantana mai kafa 40. Binciken hadin gwiwa da aka yi ya nuna akwai katon 255 na Tramadol daban daban da wasu haramtattun kwayoyin.

"Binciken ya nuna cewa wannan Tramadol din a kasar akistan aka kera su, hakan sabon lamari ne domin wadanda aka kama a baya a India aka kera su.

"Wannan lamari ne da duniya ke saka ido a kai. Safarar miyagun kwayoyi na daya daga cikin manyan abin da ke asassa rashin tsaro a yankunan kasar nan.

"Abdullah ya ce wannan babban nasara ce ga binciken da hukumar ke yi domin an gano sabuwar hanyar da ake shigo da miyagun kwayoyi daga Pakistan zuwa Turai kafin ya shigo Najeriya. "An boye kwayoyin Tramadol din ne a cikin kwalayen buroshi.

"Abdullahi ya ce zai cigaba da bincike har sai ya gano ainihin wadanda suke shigo da kwayoyin kuma ya yi kira ga sauran hukumomin tsaro su hada kai da NDLEA wurin saman nasarar binciken.

"Ya yaba da kokarin rundunar yan sanda, NAFDAC da sauran hukumomi da ke basu hadin kai wurin binciken," a cewar sanarwar.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel