Buhari ya amince da yi wa attajiran 'yan Najeriya karin kudin wutar lantarki

Buhari ya amince da yi wa attajiran 'yan Najeriya karin kudin wutar lantarki

A ranar Talata ne shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya amince da bukatar sabon tsarin kudin wutar lantarki na NESI (Nigerian Electricity Supply Industry).

Jaridar TheCable ta rawaito cewa sabon tsarin karin wutar lantarkin ba zai shafi rukunin gidajen talakawa ba.

Kazalika, shugaba Buhari ya amince da yin sassaucin biyan haraji da kaso 35% a kan sabbin mitocin wutar lantarki da za a sayo daga ketare.

A cikin watan Janairu ne hukumar kula raba hasken wutar lantarki a kasa (NERC) ta sanar da cewa za a yi karin kudin wutar lantarki a fadin kasa daga ranar 1 ga watan Afrilu.

NERC ta dakatar da kamfanonin rarraba hasken wutan lantarki (DisCos) daga shirin kara kudin wutar lantarki a cikin watan Maris saboda ballewar annobar korona.

Kazalika, a cikin watan Yuni, majalisar dattijai ta rarrashi DisCos a kan su hakura da batun kara kudin wutan lantarki har sai farkon shekarar 2021 sakamakon barkewar annobar korona a shekarar 2020.

Buhari ya amince da yi wa attajiran 'yan Najeriya karin kudin wutar lantarki
Buhari
Source: Twitter

Shugaban majalisar dattijai, Ahmad Lawan, ya bukaci a samar da mitocin lantarki na zamani ga jama'a kafin a yi karin kudin wutan lantarki.

Sabon tsarin da shugaba Buhari ya amince da shi zai fara aiki ne daga ranar 1 ga watan Satumba, sannan za a cigaba da yi masa garambawul duk bayan watanni uku.

DUBA WANNAN: Gwamnan jihar Jigawa na farko a mulkin soji ya rasu

Karin kudin na daga cikin sharudan da bankin duniya ya saka kafin bawa bangaren wutar lantarki rancen dalar Amurka $1.5bn.

A bisa sabon tsarin, masu amfani da wutar lantarki da ke kan tsarin R3 a Abuja zasu koma biyan N47.09 da N63.42 daga N27.20 da suke biya a kan kowanne yunit na wuta.

Kwastomomi da ke kan tsarin R3 a Legas zasu koma biyan N36.49 da N58 daga N26.02 da suka biya a kan owanne yunit na wuta a baya, kamar yadda kamfanin raba hasken wutar lantarki na Ikeja (IKEDC) ya sanar.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Nigeria

Online view pixel