Saboda haihuwar tagwaye: Magidanci ya tsere ya bar matarsa da 'ya'yansa

Saboda haihuwar tagwaye: Magidanci ya tsere ya bar matarsa da 'ya'yansa

- Wani mutumin kasar Uganda da aka ambata da suna Ssalongo Moses Isabirye ya gudu ya bar matarsa da yara bakwai ciki harda tagwaye uku

- Shugaban karamar hukumar Kamuli Koowa Kabatiisa ya yi bayanin cewa mutumin mai shekaru 35 ya auri Namulondo bayan mutuwar iyayenta

- Kabatiisa ya ce matar ta fuskanci kalubale da dama ciki harda rashin abinci, magani da tallafin da ya kamata

Wani mutumi mai shekaru 35 ya yasar da matarsa saboda yawan haihuwar tagwaye da take yi.

Mutumin na kasar Uganda wanda aka ambata a matsayin Ssalongo Moses Isabirye ya gudu ya bar matarsa da yara bakwai ciki harda jerin tagwaye uku.

A cewar New Vision, Isabirye ya yanke shawarar guduwa ne bayan wani likita ya bayyana cewar matarsa Lakeri mai shekaru 25 na iya haifar ‘yan uku a haihuwarta na gaba.

Shugaban karamar hukumar Koowa Kabatiisa ya tabbatar da mummunan labarin, inda ya ce mutumin mai shekaru 35 ya auri Namulondo bayan mutuwar iyayenta.

Matar mai shekaru 25 ta bayyana cewa ta bar makaranta a lokacin tana da shekaru 15, inda ta yi aure sannan ta haifi yara bakwai cikin shekaru 10.

Bayan mijinta ya gudu, sai ta koma gidan iyayenta inda take ayyukan hannu domin kula da kanta.

Sai dai kuma bata tunanin sake aure domin tana tsoron sabon mijin na iya guduwa ya barta shima.

“Ina tsoron cewa sabon mijin na iya guduwa ya bar ni,” in ji ta.

Saboda haihuwar tagwaye: Magidanci ya tsere ya bar matarsa da 'ya'yansa
Saboda haihuwar tagwaye: Magidanci ya tsere ya bar matarsa da 'ya'yansa. Hoto daga New Vision
Asali: UGC

KU KARANTA: Kano: Mata mai tsohon ciki ta rasu bayan mijinta ya garkameta na kwanaki

Sako ‘yan sanda a cikin lamarin

Namulondo wacce ta dogara a kan taimakon abokai da bayin Allah, ta ce ba za ta iya kai tsohon mijinta wajen yan sanda ba saboda matsalar kudi.

Kabatiisa ya ce matar ta fuskanci matsaloli da dama da suka hada da rashin abinci, magani da tallafi.

A wani bangare na daban, a wani rahoto da Face2Face Afrika ta ruwaito, Sarki Abumbi II na yankin Arewa maso Yammacin kasar Kamaru, yana da mata 100 da 'ya'ya 500.

Sarkin wanda yake shine Sarki na 11 a tarihin masarautar Bafut, ya hau kujerar mulki bayan mahaifinsa Sarki Achirimbi ya mutu a shekarar 1968, bayan ya zama Sarkin kabilar su ya kuma gaji mata 72 da mahaifinsa ya mutu ya bar mishi.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel