Bidiyo: Yadda aka tono wani yaro dan shekara 4 da rai bayan shafe kwana daya a karkashin wani gini da ya danne shi

Bidiyo: Yadda aka tono wani yaro dan shekara 4 da rai bayan shafe kwana daya a karkashin wani gini da ya danne shi

- An samu nasarar tono wani karamin yaro dan shekara hudu da gini ya binne mai hawa biyar a kasar Indiya da ranshi

- An tono yaron ne bayan shafe kusan kwana daya a cikin wannan burbushin gini

- Ginin dai kamar yadda aka ruwaito ya fadi a ranar Litinin inda ya danne kimanin mutane 70 a wajen

Masu taimako daga kasar Indiya sun tono wani yaro dan shekara hudu da rai daga cikin burbushin gini da ya danne shi tsawon kwana daya yana karkashi.

Mutane sunyi ta murna a ranar Talata 25 ga watan Agusta, bayan an toni yaron daga karkashin ginin da ya danne shi mai hawa biyar, bayan yaron, ginin kuma ya danne mutum 70 a wajen.

Bidiyo: Yadda aka tono wani yaro dan shekara 4 da rai bayan shafe kwana daya a karkashin wani gini da ya danne shi
Bidiyo: Yadda aka tono wani yaro dan shekara 4 da rai bayan shafe kwana daya a karkashin wani gini da ya danne shi
Asali: Facebook

Lamarin dai ya faru a ranar Litinin 24 ga watan Agusta, a yammacin garin Mahad, dake kudancin Mumbai.

Sai da aka sanya ma'aikata da yawan gaske da kuma karnuka masu jiyo kamshin abu, inda suka yi ta aiki har zuwa cikin dare suna dauke da bulo da kwanika duka wajen neman wadanda ke da kwana a gaba.

Bidiyon masu aikin ceton ya nuna yadda mutane ke ta faman yaba musu yayin da suka zaro yaron daga cikin wannan burbushin duwatsu da suka danne shi.

KU KARANTA: Hotuna: Kamfanin mota na Najeriya ya gwangwaje hukumar 'yan sanda da motoci masu dan karen kyau

Kakakin jami'an da suke aikin ceton Sachidanand Gawde ya bayyanawa manema labarai cewa ma'aikatansu sun tono gawarwakin mutane biyu, ciki hadda wannan karamin yaro da aka tarar a raye.

Da farko dai, wani jami'i ya sanar da kamfanin dillancin labarai cewa ma'aikatan ceton sun tono sama da mutane 60 da ran su daga cikin wannan wuri.

A kasa dai bidiyon lokacin da aka tono yaron ne daga cikin wajen, inda mutane ke ta murna.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel