Zamu sake tsunduma ma'aikata 774,000 da zamu dauka cikin harkar noma bayan kammala aikinsu na wata uku - Gwamnatin tarayya

Zamu sake tsunduma ma'aikata 774,000 da zamu dauka cikin harkar noma bayan kammala aikinsu na wata uku - Gwamnatin tarayya

- Gwamnatin tarayya ta sake bayyana abubuwan da za tayi da ma'aikata 774,000 da za ta dauka

- Hukumar daukar ma'aikatan ta ce ba zata sallami ma'aikatan ba bayan sun kammala watanni ukun da za su yi

- Darakta janar, Mohammed Argungu, ya ce zasu tsunduma ma'aikatan harkar noma ne da zarar sun kammala aikinsu

Darakta Janar na hukumar daukar ma'aikata ta kasa, Mohammed Nasir Ladan Argungu, ya bayyana cewa ma'aikata 774,000 da za a dauka baza a sallame su ba bayan sun kammala aikinsu na watanni uku.

Daraktan ya ce, za a tsunduma ma'aikatan ne cikin harkar noma, inda hakan ya kawo karshen kace-nacen da ake yi akan daukar aikin.

Da yake hira da Daily Trust, Argungu wanda yake shine shugaban kwamitin daukar ma'aikatan na kasa, ya ce akwai mutanen da suke kokari wajen bata wannan shiri.

Zamu sake tsunduma ma'aikata 774,000 da zamu dauka cikin harkar noma bayan kammala aikinsu na wata 3
Zamu sake tsunduma ma'aikata 774,000 da zamu dauka cikin harkar noma bayan kammala aikinsu na wata 3
Asali: Facebook

Ya kara da cewa takun sakar da aka samu kwanakin baya kan daukar aikin ya biyo bayan bambancin ra'ayi da aka samu tsakanin 'yan majalisar tarayya da suke so a danka musu komai a hannu.

Argungu ya ce gwamnatin tarayya, da ma'aikatar ayyuka da samar da ayyukan yi ta kasa, baza ta bari wasu su bata wannan shiri ba.

Ya kara da cewa idan aka samu nasara komai ya tafi yadda ake so, wannan shiri zai kawo cigaba a fannin tattalin arziki, zai samar da ayyukan yi da kuma rage talauci a tsakanin al'umma.

KU KARANTA: Sunaye: Jam'iyyar PDP ta ware kwamiti ta mutum 145 da zasu yi yakin neman zaben gwamnan jihar Ondo

"Na yadda cewa wannan shiri ne mai matukar muhimmanci. Ba wai kawai iya daukar ma'aikata 1,000 kawai za ayi a kowacce karamar hukuma ta kasar nan ba.

"Mun gabatar da bincike na musamman a fadin Najeriya, zamu yi amfani da wadannan ma'aikata da zamu dauka wajen sanya su cikin harkar noma bayan kammala aikin na watanni uku. Mun riga mun gama shirin komai," cewar Argungu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel