Sunaye: Jam'iyyar PDP ta ware kwamiti ta mutum 145 da zasu yi yakin neman zaben gwamnan jihar Ondo
- PDP ta bayyana sunayen mutum 145 da za su yi yakin neman zaben gwamnan jihar Ondo
- Jam'iyyar ta bayyana gwamnan jihar Oyo, Seyi Makinde a matsayin shugaban kwamiti
- Manyan mutane a cikin jerin 'yan kwamitin sun hada da Bello Matawalle, Nyesom Wike da kuma wasu manyan 'yan jam'iyya
Babbar jam'iyyar adawa ta PDP ta bayyana 'yan kwamitin yakin zaben gwamnan jihar Ondo wanda za a gabatar a watan Oktoba.
A wata sanarwar da jam'iyyar ta fitar a yau Laraba, 26 ga watan Agusta, ta bakin mai magana da yawunta Kola Ologbondiyan, ta bayyana gwamna Seyi Makinde na jihar Oyo a matsayin shugaban kwamitin.
Haka kuma jam'iyyar adawar ta bayyana gwamna Bello Matawalle na jihar Zamfara a matsayin mataimakin shugaban kwamitin, haka kuma jerin 'yan kwamitin 145 ya nuna Malam Abdullahi Maibasira a matsayin sakataren kwamitin.
KU KARANTA: Hotuna: Labarin Sarki Abumbi na nahiyar Afrika dake da mata 100 da 'ya'ya 500
PDP ta ce zata kaddamar da wannan kwamiti ta neman zabe a ranar Juma'a 28 ga watan Agusta, a sakatariyar jam'iyyar dake babban birnin tarayya Abuja, ta hanyar amfani da manhajar waya sakamakon annobar coronavirus.
Sauran manya daga cikin 'yan kwamitin sun hada da gwaman Nyesom Wike na jihar Ribas, gwamna Aminu Tambuwal na jihar Sokoto, gwamna Benedict Ayade na jihar Cross River, da kuma gwamna Ahmadu Fintiri na jihar Adamawa.
Sauran sun hada da gwamna Godwin Obaseki na jihar Edo, gwamna Darius ishaku na jihar Taraba, gwamna Okezie Ikpeazu na jihar Abia da kuma wasu daga cikin manyan 'yan jam'iyya.
Hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta (INEC) ta bayyana ranar 10 ga watan Oktoba 2020 a matsayin ranar zaben gwamnan jihar ta Ondo.
PDP da ta bayyana Eyitayo Jegede (SAN) a matsayin dan takararta bayan ya lashe zaben fidda gwani na jam'iyyar, akwai yiwuwar za ta gasawa jam'iyyar APC mai mulki aya a hannu a wannan karon.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng