Daga cewa mijina bana jin dadi, sai ya fita dawowar da zai yi ya siyo mini sabuwar mota - Matar aure ta bayyana yadda mijinta yayi mata goma ta arziki

Daga cewa mijina bana jin dadi, sai ya fita dawowar da zai yi ya siyo mini sabuwar mota - Matar aure ta bayyana yadda mijinta yayi mata goma ta arziki

- Wani dan Najeriya ya bawa matarshi wacce bata jima da haihuwa ba sabuwar mota

- Matar ta karbi motar cikin matukar farin ciki, inda bakinta ya kasa rufuwa

- Sakamakon wannan tsagwaron soyayya da mijin ya nunawa matar ya sanya mutane suka yi ta yaba masa

Wani mutumi dan Najeriya wanda ke da shafin Twitter mai suna @AdesojiMinkail ya yiwa matarsa kyautar sabuwar mota.

Kafin ya bata kyautar motar ya shigo da ita zuwa gidan a cikin daren ba tare da ya sanar da ita ba. Washe gari sai ya kirata waje ya nuna mata.

Daga cewa mijina bana jin dadi, sai ya fita dawowar da zai yi ya siyo mini sabuwar mota - Matar aure ta bayyana yadda mijinta yayi mata goma ta arziki
Daga cewa mijina bana jin dadi, sai ya fita dawowar da zai yi ya siyo mini sabuwar mota - Matar aure ta bayyana yadda mijinta yayi mata goma ta arziki
Asali: Facebook

Ai kuwa da ganin wannan kyakkyawar mota ya sanya ta kasa magana saboda tsananin murna.

A ranar Lahadi, 23 ga watan Agusta, mutumin yayi rubutu kamar haka: "Bari mu gani lokacin da zata dauka kafin ta gano."

KU KARANTA: Hotunan jiragen kasa na zamani guda 11 da za a kawo Najeriya daga kasar China

Haka kuma daga baya ya wallafa bidiyon yadda ya bata kyautar motar da kuma yadda matar tayi rike da diyarsu a hannu.

Mutane da yawa sunyi ta yaba mishi akan sanya farin ciki da yayi a zuciyar wannan mata, inda suka yi ta yi masa addu'a.

A wani labari kuwa ita kuma wata mata ce ta mayar da naira miliyan sha hudu (N14m) da aka yi kuskuren turawa cikin asusunta.

Matar mai suna Josephine Nchetaka Chukujama Eze, ta nuna ainahin adalci bayan ta mayar da kimanin naira miliyan goma sha hudu da aka yi kuskuren aikawa zuwa asusunta na banki.

Mijinta wanda yake dan jarida ne kuma lauya, Chukujama Eze, ya bayyana haka ga News Express yayin da yake yabon matarshin akan abin kirkin da tayi.

Ga dai cikakken rahoton: Ba a rasa na Allah: Matar aure ta mayar da naira miliyan 14 da aka yi kuskuren tura mata ta banki

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel