Zargin neman mata: Matar aure ta wanke mijinta da acid, alkali ya daureta

Zargin neman mata: Matar aure ta wanke mijinta da acid, alkali ya daureta

Wata kotun Majistare da ke garin Osogbo, a jihar Osun, a ranar Talata ta bukaci a tsare mata wata matar aure mai shekaru 44 a duniya mai suna Adetoro Olawuni, a gidan gyaran hali.

Ana zargin Adetoro da watsa wa mijinta mai suna Olapoju Olawuni acid, lamarin da ya kona shi ba kadan ba.

Dan sandan mai gabatar da kara, ASP Abiodun Fagboyinbo, ya sanar da kotun cewa, Adetoro ta aikata laifin a ranar 12 ga watan Satumban 2017 wurin karfe 1 na dare a yankin Prime da ke Osogbo.

Bayan yin aika-aikar, Adetoro ta tsere inda daga bisani aka damketa a ranar Litinin.

Fagboyinbo ya sanar da kotun cewa, Olawuni ya matukar shan wahala sakamakon kunar kuma ya kasance yana yawon asibiti a jihar Edo.

Baya ga nan, an yi masa aiki daban-daban a jikinsa amma har a halin yanzu bai warke ba.

Duk da dan sandan bai bayyana abinda ya assasa rigima tsakanin ma'auratan ba, Daily Trust ta gano cewa mai kare kanta ta zargi mijinta da ajiye karuwa a waje bayan yana da aure.

Zargin neman mata: Matar aure ta wanke mijinta da acid, alkali ya daureta
Zargin neman mata: Matar aure ta wanke mijinta da acid, alkali ya daureta. Hoto daga The Nation
Asali: Twitter

KU KARANTA: Yanzu-yanzu: Buhari ya shiga muhimmiyar ganawa da Buni da Ganduje

Adetoro bata amsa dukkan laifukan da ake zarginta da su ba, amma lauyanta mai suna Okobe Najite ya mika bukatar karbar belin wacce yake karewa.

Amma, Fagboyinbo ya soki wannan bukatar inda ya ja kunnen cewa wacce ake zargin za ta iya tsallake sharuddan belin.

Alkalin kotun, Abayomi Ajala, ya bukaci a tsare masa Adetoro a gidan gyaran hali da ke Ilesa har zuwa ranar Talata, 8 ga watan Satumba don ci gaba da shari'ar.

A wani labari na daban, wata shakatawar soyayya da aka fita a Mt Hampden ta tashi da alhini tare da jimami a kasar Zimbabwe, shafin Linda Ikeji ya wallafa.

Christopher Muchenga mai shekaru 49 ya sheka lahira bayan karuwarsa ta tsinke masa mazakuta sakamakon rikicin da ya shiga tsakaninsu.

Karuwar magidancin an gano sunanta Mbuya Ropafadzo, kuma an gano lamarin ya auku ne a makon da ya gabata.

Muchenga ya rasu ne bayan tsinke masa mazakuta da karuwar tayi bayan kayar da shi kasa da tayi sakamakon rikicin da ya shiga tsakaninsu.

Mai magana da yawun iyalansa, Margaret Kamwaza, ta ce ya yanke hukuncin samun lokacin shakawata da Mbuya Ropafadzo bayan karbar albashinsa amma sai lamarin ya kasance haka.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel