Amarya ta rabu da mijinta bayan ta gano cewa aikin kwasar bola yake yi bayan yayi mata karyar cewa shi ma'aikacin jirgin sama ne

Amarya ta rabu da mijinta bayan ta gano cewa aikin kwasar bola yake yi bayan yayi mata karyar cewa shi ma'aikacin jirgin sama ne

- Shamim dai abinda ta sani shine mijinta yana aiki a filin jiragen sama na Jomo Kenyatta, har zuwa lokacin da gaskiya tayi halinta

- Bayan ta hadu da makwabtanta sunyi ta yi mata dariya akan ta auri mai kwasar shara

- Daga baya Shamim ta tilasta mijinta ya gaya mata gaskiya, inda a karshe ta raba auren dake tsakaninsu

- Mijin nata mai suna David ya bita gidansu domin neman ta yafe masa bayan auren nasu ya rabu

Wata mata da ta fito daga yankin Embakasi mai suna Shamim ta bayyana dalilan da ya sanya baza ta yafewa mijinta ba.

A wata hira da tayi da wani mai suna Anthony Ndiema a wani shiri mai suna Nisamehe Show, matar ta bayyana cewa mijinta ya zabga mata karya wacce ta kasa hakuri da shi bayan ta gano gaskiya.

Shamim ta bayyana cewa ita abinda ta sani shine mijinta ma'aikacin filin jirgin sama ne, har zuwa lokacin da ta hadu da makwabtanta a lokacin ne ta gano gaskiya.

Amarya ta rabu da mijinta bayan ta gano cewa aikin kwasar bola yake yi bayan yayi mata karyar cewa shi ma'aikacin jirgin sama ne
Amarya ta rabu da mijinta bayan ta gano cewa aikin kwasar bola yake yi bayan yayi mata karyar cewa shi ma'aikacin jirgin sama ne
Asali: Facebook

"Yana barin gida da safe cikin kaya masu kyau da mutum ba zai taba iya ganewa ba. To muna rikici da makwabtana akan ruwa sai daya daga cikinsu take ce mini babu yadda za ayi na fita daban bayan mijina aikin diban bola yake. Nayi kokarin kare mijina saboda nasan cewa mijina ba abinda yake yi ba kenan, sai naji sauran suna goya mata baya, sai na gano cewa akwai alamun gaskiya a ciki," ta ce.

KU KARANTA: Kwamacala: Matar aure ta gaji da zama da mijinta ta fita taje tana soyayya da mata da miji a lokaci guda

Bayan David ya dawo gida, Shamim ta tilasta shi akan ya gaya mata gaskiya, inda a karshe ya sanar da ita gaskiyar lamarin.

Amarya ta rabu da mijinta bayan ta gano cewa aikin kwasar bola yake yi bayan yayi mata karyar cewa shi ma'aikacin jirgin sama ne
Amarya ta rabu da mijinta bayan ta gano cewa aikin kwasar bola yake yi bayan yayi mata karyar cewa shi ma'aikacin jirgin sama ne
Asali: Facebook

Shamim ta ce mijinta ya kware wajen karya, domin kuwa badan haka ba baza ta taba ganowa ba; hatta iyayenta sun dauke shi a matsayin ma'aikacin filin jirgin sama.

Ta ce ta rabu da shine ba wai saboda aikin bane, sai don karyar da yayi mata da kuma kunya da ya sanya taji a idon duniya.

A bidiyon, Anthony ya roki Shamim akan tayi magana da David taji dalilin shi nayin karyar.

A wayar da suka yi, David ya ce ya san cewa abinda yayi bai kyauta ba, kuma yayi hakane saboda ya kare soyayyarsa da kuma iyalin shi.

"Inda ace bana sonki babu yadda za'ayi na baki hakuri, amma duk da haka ina so ki yafe mini bisa karyar dana yi miki , ina kuma fatan zaki amince mu koma kamar yadda muke a baya," ya ce.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel