Hotuna: Labarin Sarki Abumbi na nahiyar Afrika dake da mata 100 da 'ya'ya 500

Hotuna: Labarin Sarki Abumbi na nahiyar Afrika dake da mata 100 da 'ya'ya 500

- Sarki Abumbi II dake yankin Arewa maso Yammacin kasar Kamaru, yana da mata 100 da 'ya'ya 500

- Rahotanni sun nuna cewa ya auri mata 28 da kansa, inda sauran mata 72 kuma ya gaje su ne a wajen mahaifinsa, Sarki Achirimbi

- Matan Sarkin ba wai a baki kawai suke mata ba, suna da karfin iko sosai a yankin

A wani rahoto da Face2Face Afrika ta ruwaito, Sarki Abumbi II na yankin Arewa maso Yammacin kasar Kamaru, yana da mata 100 da 'ya'ya 500.

Sarkin wanda yake shine Sarki na 11 a tarihin masarautar Bafut, ya hau kujerar mulki bayan mahaifinsa Sarki Achirimbi ya mutu a shekarar 1968, bayan ya zama Sarkin kabilar su ya kuma gaji mata 72 da mahaifinsa ya mutu ya bar mishi.

Hotuna: Labarin Sarki Abumbi na nahiyar Afrika dake da mata 100 da 'ya'ya 500
Hotuna: Labarin Sarki Abumbi na nahiyar Afrika dake da mata 100 da 'ya'ya 500
Asali: Facebook

Wadannan mata da ya gada daga wajen mahaifinsa ya kara su akan 28 da ya riga ya aura, inda suka zama guda 100. A wata hira da yayi da manema labarai, matarshi ta uku Sarauniya Constance ta ce: "A tare da kowanne namiji da ya zama wani abu a rayuwa akwai mace a tare da shi."

"Al'adar mu ta amince idan kana Sarki tsofaffin matanka su barwa kananan komai, sannan kuma su koyawa Sarkin al'adu saboda Sarkin a baya Yarima ne ba Sarki ba."

An gano cewa Sarauniyar tana da ilimi sosai, har ma tana iko sosai a masauratar.

KU KARANTA: Hotunan jiragen kasa na zamani guda 11 da za a kawo Najeriya daga kasar China

Hotuna: Labarin Sarki Abumbi na nahiyar Afrika dake da mata 100 da 'ya'ya 500
Hotuna: Labarin Sarki Abumbi na nahiyar Afrika dake da mata 100 da 'ya'ya 500
Asali: Facebook

Hotuna: Labarin Sarki Abumbi na nahiyar Afrika dake da mata 100 da 'ya'ya 500
Hotuna: Labarin Sarki Abumbi na nahiyar Afrika dake da mata 100 da 'ya'ya 500
Asali: Facebook

Sarki Abumbi ya ce matan shi suna da matukar muhimmanci a wajen shi, inda kuma yayi magana akan hada al'adarsu da zamani saboda a rage samun matsala.

Fadarshi ta zama wajen yawon bude ido, kuma an sanyata a cikin wuraren da suka fi hatsari a duniya.

Duk da dai a wannan zamanin ba a dauki sarautar gargajiya da muhimmanci ba, amma har yanzu ya zama mai fada a ji a gwamnatin kasar Kamaru.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel