Bayan karbar albashi, ya tafi shakatawa da karuwarsa inda ta tsinke masa mazakuta sakamakon rikici

Bayan karbar albashi, ya tafi shakatawa da karuwarsa inda ta tsinke masa mazakuta sakamakon rikici

- Bayan karbar albashin wani aiki da Christopher Muchenga ya yi, ya yanke shawarar samun lokacin soyayya da masoyiyarsa

- Sun kwashe tsawon dare suna shakatawa inda daga bisani suka yanke hukuncin komawa gida, lamarin da ya kawo rikici tsakaninsu

- Makwabta sun tabbatar da sun ji lokacin da suke fada kuma ta kayar da shi kasa tare da tsinke masa mazakuta har yace ga garinku

Wata shakatawar soyayya da aka fita a Mt Hampden ta tashi da alhini tare da jimami a kasar Zimbabwe, shafin Linda Ikeji ya wallafa.

Christopher Muchenga mai shekaru 49 ya sheka lahira bayan karuwarsa ta tsinke masa mazakuta sakamakon rikicin da ya shiga tsakaninsu.

Karuwar magidancin an gano sunanta Mbuya Ropafadzo, kuma an gano lamarin ya auku ne a makon da ya gabata.

Muchenga ya rasu ne bayan tsinke masa mazakuta da karuwar tayi bayan kayar da shi kasa da tayi sakamakon rikicn da ya shiga tsakaninsu.

Mai magana da yawun iyalansa, Margaret Kamwaza, ta ce ya yanke hukuncin samun lokacin shakawata da Mbuya Ropafadzo bayan karbar albashinsa amma sai lamarin ya kasance haka.

Bayan karbar albashi, ya tafi shakatawa da karuwarsa inda ta tsinke masa mazakuta sakamakon rikici
Bayan karbar albashi, ya tafi shakatawa da karuwarsa inda ta tsinke masa mazakuta sakamakon rikici. Hoto daga shafin Linda Ikeji
Asali: Twitter

KU KARANTA: Kiri-kiri: Yadda aka kama Maigadi yana yi wa yarinya mai shekaru 8 fyade (Hotuna)

Ta ce: "Mun rasa dan uwa mai kaunarmu kuma yadda ya rasu ne abun da yafi kona mana rai. Ya so kyautatawa masoyiyarsa ne bayan ya karba albashinsa wanda yakamata ya yi wa iyalansa amfani da su.

“An gano cewa ya karba albashin ne bayan wani aiki da yayi, amma sai ya je shakatawa da masoyiyarsa.

“Sun kwashe tsawon daren tare amma bayan isarsa gidanta, an gano sun fara hayaniya wacce ta tada makwabta daga bacci.

"Masoyiyar tasa ta tsinke masa gabansa bayan kayar da shi kasa da tayi, inda a take ya ce ga garinku."

An zargi cewa, bayan da Muchenga ya mutu, Ropafadzo ta ja gawarsa zuwa bakin kofa inda ta kira 'yan sanda tare da ikirarin cewa ta samu gawarsa a gaban kofarta kuma bata san shi ba.

Muchenga ya rasu ya bar 'ya'ya hudu a duniya.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel