Hotunan jiragen kasa na zamani guda 11 da za a kawo Najeriya daga kasar China

Hotunan jiragen kasa na zamani guda 11 da za a kawo Najeriya daga kasar China

- Za a kawo jiragen kasa na zamani guda 11 Najeriya daga kasar China wadanda zasu dinga jigilar fasinjoji daga Abuja zuwa Kaduna da kuma Legas zuwa Ibadan

- Labarin shigo da kayuwan jiragen ya fito daga kamfanin na kasar China mai suna CRRC Corporation Ltd, wadanda sune suke da alhakin gina hanyar dogon a Najeriya

Titin dogo da aka gina daga Legas zuwa Ibadan wanda zai fara aiki a watan Satumbar da zamu shiga, an sanya ranar fara aikin akan gaba domin kuwa akwai sababbin kayuwan jiragen kasa da suke kan hanya daga kasar China.

Shafin kamfanin CRRC Corporation Ltd, dake aikin gina hanyar jiragen kasar a Najeriya shine ya wallafa labarin shigo da jiragen a shafinsu na Twitter a ranar Litinin 25 ga watan Agusta.

Hotunan jiragen kasa na zamani guda 11 da za a kawo Najeriya daga kasar China
Hotunan jiragen kasa na zamani guda 11 da za a kawo Najeriya daga kasar China
Asali: Facebook

A cewar rahoton da kamfanin ya wallafa, sababbin kayuwan jiragen za a kara su akan wadanda suke aiki daga Abuja zuwa Kaduna.

A yanzu haka dai kayuwan jiragen sun bar tashar jirgin ruwa ta Changzhou sun isa Shanghai, za kuma su iso Najeriya nan da 'yan kwanaki. Wannan labari da kamfanin ya wallafa ya jawo kace nace sosai a Twitter, inda kowa ke fadin albarkacin bakinsa.

KU KARANTA: Kwamacala: Matar aure ta gaji da zama da mijinta ta fita taje tana soyayya da mata da miji a lokaci guda

Yayin da wasu ke yabawa kokarin gwamnati akan irin cigaban da take kawowa Najeriya, wasu kuwa sun samu abin kushewa.

Wani mai suna @ashir_nee, cewa yayi: "Shin mai yasa 'yan Najeriya baza su ga dan kokarin da gwamnati take yi ba, kai koda ace da gawayi jiragen ke amfani muna son su a haka, maimakon komawa baya mun samu cigaba koyaya ne."

Inda shi ma wani mai suna @SteelsTobico ya ce: "Abu yayi kyau, koma yayane idan daya ya gaji za a iya canjawa da ni, bayan haka kuma kowanne abu yana da muhimmanci da kuma rashin muhimmanci."

Wani kuwa mai suna @Emmylexxz cewa yayi: "Wadannan ai sun riga sun mutu."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel