Ministan Wasanni Aisha Buhari ta so a nada Amokachi – Gara-Gombe

Ministan Wasanni Aisha Buhari ta so a nada Amokachi – Gara-Gombe

Tsohon shugaban kungiyoyin kwallon kafa ta Gombe, Shuaib Gara-Gombe ya bayyana cewa Aisha Buhari, matar Shugaba Muhammadu Buhari ta so a nada tsohon dan wasan Super Eagles, Daniel Amokachi a matsayin ministan wasanni.

A ranar 20 ga watan Agusta ne Buhari ya nada tsohon dan wasan na Everton a matsayin mataimakinsa na musamman a bangaren wasanni, watanni kadan bayan an nada shi jakadar wasanni na kasar.

Gara-Gombe, yayin hira da aka yi da shi a gidan rediyo na Kennis 104.1 FM a ranar Litinin ya ce, "Aisha Buhari ta dade tana fafutikan ganin an saka wa wadanda suka bada gudun mawa yayin yakin neman zaben mijinta, ta dade tana neman a saka wa Amokachi.

Ministan Wasanni Aisha Buhari ta so a nada Amokaci – Gara-Gombe
Ministan Wasanni Aisha Buhari ta so a nada Amokaci – Gara-Gombe
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Hotuna: Jirgin saman da ya yi karo da katanga a Legas

"Hasali ma, Ministan wasanni ta so a nada Amokaci, amma hakan bai yi wu ba, da aka cigaba da yi wa fadar shugaban kasa matsin lamba kan batun, sai Buhari ya nada shi wakilin wasan kwallo.

"Bayan nadin an ce ya rika aiki karkashin Sunday Dare. Amma kawai zuwa maaikatar ya ke yi baya aikata komai bayan nadinsa a matsayin wakilin kwallon kafa.

"Ya kamata a yi wa Amokaci sakayya. Buhari bai san Amokaci ba, amma Buhari ya san matarsa wacce ita kuma ta yi aiki tare da Amokachi a lokacin yakin neman zabensa.

"Mun dade muna kira cewa a rika nada mutane masu kwarewa a fannin wasanni mukamai da suka shafi wasanni idan ana son samun cigaba amma tsirarun da aka nada ba su tabuka komai ba ko kuma ba su cancanci nadin da aka musu ba."

A baya Legit.ng ta kawo muku cewa Shugaba Buhari ya na Daniel Amokachi a matsayin mai taimaka masa na musamman a kan harkokin wasanni.

Sanarwar da ofishin watsa labarai na Ministan Matasa da Cigaban Wasanni, Sunday Dare, ta fitar ya ce an nada shi ne a ranar 17 ga watan Agustan 2020 kamar yadda wasikar mai dauke da sa hannun sakataren gwamnatin tarayya, Boss Mustapha ta nuna.

Wani sashi na wasikar ya ce, "Ina farin cikin sanar da kai cewa, Shugaban Tarayyar Najeriya, Muhammadu Buhari ya amince da nadin ka a matsayin mai taimakawa na musamman a kan harkokin wasanni.

"Nadin zai fara aiki daga ranar 11 ga watan Agustan shekarar 2020.”

A matsayinsa na mataimaki na musamman, ana sa ran Amokaci zai rika bawa shugaban kasa shawarwari a dukkan harkokin da suka shafi wasanni.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel