Dumu-dumu: An kama kwamandan Hisbah da laifin safarar kananan yara a Kano

Dumu-dumu: An kama kwamandan Hisbah da laifin safarar kananan yara a Kano

- Shugaban hukumar yaki da safarar mutane (NAPTIP), na jihar Kano, Shehu Umar, ya ce hukumarsu ta damke kwamandan Hisbah

- Kamar yadda yayi bayani, hukumar ta cafke shugaban Hisbah ne sakamakon zarginsa da ake da hannu a siyar da wani yaro dan shekara daya

- Yaron da ake magana a kai an haifesa ne ba tare da aure ba kuma an tsincesa a Fagge, an mika shi hannun Mai Unguwa wanda suka hada kai da kwamandan suka siyar da shi

Kwamandan hukumar Hisbah na yankin Fagge, Ustaz Jamilu Yusuf, ya shiga hannun jami'an hukumar yaki da safarar mutane (NAPTIP), a kan zarginsa da ake da hannu a safarar wani yaro mai shekara daya.

Kwamandan rundunar NAPTIP na yankin, Shehu Umar, ya bayyana hakan a ranar Litinin yayin da mambobin kwamitin bincike a kan hukuncin da shari'a ta dauka a kan mutanen da suka bata a Kano suka kai masa ziyara.

Ya ce, mutum biyar hukumar ta damke har da kwamandan Hisbah, wadanda ake zargi da hannunsu a ciki.

Hukumar har a halin yanzu tana bincike kafin ta dauka matakin da ya dace a kan sacewa da siyar da yaron.

Dumu-dumu: An kama kwamandan Hisbah da laifin safarar kananan yara a Kano
Dumu-dumu: An kama kwamandan Hisbah da laifin safarar kananan yara a Kano. Hoto daga Daily Trust
Asali: Facebook

KU KARANTA: Sanusi ya yi martani a kan janye gayyatar El-Rufai da NBA ta yi daga taronta

Jaridar Daily Trust ta gano cewa, dan da ake zargin jama'ar da sacewa an haifeshi ne ba tare da aure ba, kuma mahaifiyarsa ce ta yasar da shi a Fagge, kusan shekara daya da ta gabata.

A yayin da aka samo yaron, an mika shi hannun Mai unguwan Fagge kafin a siyar da shi kamar yadda ake zargi ga wata mata 'yar asalin jihar Imo, asalin garinsu kwamandan.

Daga Mai Unguwar har matar da ake zargi ta siya yaron an kama su, kuma suna hannun hukumar NAPTIP inda suke fuskantar tuhuma.

Kwamandan ya ce za a gurfanar da wadanda ake zargi a gaban kotu bayan sun kammala binciken lamarin.

Shugaban kwamitin, Mai shari'a Wada Umar, ya ce ziyarar da suka kai sun yi ta ne don habaka hadin guiwa tare da kokarin shawo kan matsalar batan jama'a a jihar.

Hisbah hukuma ce ta 'yan sandan Musulunci wacce ke da alhakin tabbatar da dokokin shari'a a tsakanin Musulmi a jihar.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel