Bidiyon Jessica Cox, mutum ta farko a duniya da take tuka jirgin sama da kafa

Bidiyon Jessica Cox, mutum ta farko a duniya da take tuka jirgin sama da kafa

- Jessica Cox, wacce ta kammala karatu a bangaren karantar dan adam, ta zama direbar jirgi ta farko mai lasisi a duniya da take tuki da kafa

- Bayan haifarta da nakasa, tana yin komai da kafarta, kuma har ta ciyo kambu na damben Taekwando

Cewar abu baya yiwuwa a rayuwa ya zama tarihi a yanzu. Labarin Jessica Cox ya zama haka. Duk da cewa an haifeta ba tare da hannu ba, hakan bai hanata cimma burinta na rayuwa ba.

Bidiyon Jessica Cox, mutum ta farko a duniya da take tuka jirgin sama da kafa
Bidiyon Jessica Cox, mutum ta farko a duniya da take tuka jirgin sama da kafa
Asali: UGC

Ta samu nasarar lashe kambun dambe na Taekwando, sannan kuma tana yin duk wasu abubuwa na rayuwarta da kafa kamar dai yadda mai hannu ke yi. Haka tana yin kida na Piano, abu da yafi banbanta ta da kowa shine, ita ce mace ta farko da ta samu lasisin tukin jirgin sama ba tare da hannu ba.

Jessica ta ce mutane da yawa suna kallon rashin hannunta a matsayin wata babbar nakasa, amma ta basu mamaki da abubuwan da take yi.

KU KARANTA: Mace mai kamar maza: Ta yi watsi da daukar 'yan aiki ta zage dantse tana gina gidanta da kanta

Mijinta ya ce idan zai misalta matarshin a cikin kalma uku shine, zai ce ita mai kirki ce, mai hangen nesa, sannan kuma babu abinda ke sawa ta ja baya. Jessica ta shiga harkar tukin jirgin sama a lokacin da wani direban jirgin yaki na soja ya tambayeta ko tana so ta koya.

Ga dai bidiyonta a kasa:

Jessica ta samu lasisinta a ranar 10 ga watan Oktobar shekarar 2008, bayan ta shafe shekara uku tana koyon tukin jirgin.

Jessica dai ta kammala karatu a fannin karantar halayen dan adam a jami'ar Arizona a shekarar 2005.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel