Yanzu-yanzu: Gwamna Buni ya sasanta Amaechi da Sylva
A cikin kokarin kwamitin sasanci na rikon kwarya na jam'iyyar APC wanda ya samu jagorancin Gwamna Mai Mala Buni, a ranar Litinin an yi nasarar sasanta ministan sufuri, Rotimi Amaechi da takwaransa, karamin ministan man fetur, Timipre Sylva.
Dukkan ministocin sun amince za su yi aiki tare don kawo gyara a jam'iyyar a yankin kudu-kudun kasar nan.
Amaechi ya taba yin gwamnan jihar Ribas, hakazalika Sylva ya taba zama gwamnan jihar Bayelsa.
A yayin bayanin wannan ci gaban ga manema labarai, bayan tattaunawar sirri da aka yi tsakanin tsoffin gwamnonin da shugaban kwamitin rikon kwaryar a babban ofishin jam'iyyar APC a Abuja, sun tabbatar da sasancin.
Tun farko, ministan sufuri ya isa sakateriyar wurin karfe 1:15 na rana, kuma ya bar wurin bayan mintoci kadan.
Ya dawo tare da shugaban kwamitin rikon kwarya na jam'iyyar inda karamin ministan man fetur din ya iskesu wurin karfe 2 na rana, sannan suka shiga ganawar sirri wacce ta dauka tsawon sa'a daya.
Banbancin siyasa da ke tsakanin shugabannin jam'iyyar APC na kudancin ya kawo baraka ga zabukan jam'iyyar a yankin.
A yayin bayani ga manema labarai bayan ganawar sirrin, Amaechi wanda suka rankayo tare da tsohon gwamnan Sylva, ya ce: "Mun amince za mu yi aiki tare domin ci gaban jam'iyyar."
KU KARANTA: Abubuwa 3 da suka kawo Muhammadu Sanusi II arewa
Karin bayani yana nan tafe...
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng