Gyaran asibitoci: Hadimin Shugaban kasa ya kare Aisha Buhari daga sukar masu suka

Gyaran asibitoci: Hadimin Shugaban kasa ya kare Aisha Buhari daga sukar masu suka

- Hadimin Shugaban kasa, Aliyu Abdullahi ya kare Uwargida Aisha Buhari

- Mai dakin Shugaba Muhammadu Buhari ta fito ta na kiran a gyara asibitoci

- Abdullahi ya kira masu sukar Hajiya Buhari da munafukai da makiyan kasa

Daya daga cikin mukarraban shugaban Najeriya, Aliyu Abdullahi, ya dura kan wadanda su ke sukar kalaman da Aisha Muhammadu Buhari ta yi kwanan nan.

Hajiya Aisha Muhammadu Buhari ta yi kira ga gwamnati ta inganta harkar kiwon lafiya a Najeriya ta hanyar gyara asibitoci, domin a rage zuwa fita kasashen waje.

Wannan kira da uwargidar shugaban kasar ta yi bai yi wa wasu dadi ba, ganin cewa ta yi wannan jawabi ne daga sa kafarta a Najeriya bayan ta dawo daga asibiti a ketare.

Aliyu Abdullahi wanda hadimin shugaban kasa Muhammadu Buhari ne ya kare uwargidar mai gidansa, ya ce masu sukar Aisha Buhari munafukai ne kuma makiyan kasa.

A wani jawabi da ya yi a shafin Twitter a ranar Litinin, 24 ga watan Agusta, Abdullah ya ce ba a kan Buhari farau ba, iyalan tsofaffin shugabannin kasa duk su kan yi wannan.

KU KARANTA: Jihohi su nemi hanyar samun kudi, abubuwa sun yi wa asusun FAAC nauyi

Gyaran asibitoci: Hadimin Shugaban kasa ya kare Aisha Buhari daga sukar masu suka
Aisha Buhari ta na so a gyara asibitoci Hoto: Twitter
Asali: Facebook

“Masu zagin uwargida, @aishambuhari saboda ta yi ta-maza, ta yi kiran gaskiya, ta na neman a ayi wani abu domin rage fita asibitin kasashen waje, ganin abin da ya faru da ita kwanan nan, ta ga likita a wajen Najeriya, su ne ainihin makiyan kasar nan, kuma munafukai.”

Mai taimakawa shugaban kasar wajen yada labarai ya kara da: "Shugabannin baya da masu-ci da iyalansu duk su na yin wannan a ko yaushe, amma ba za su taba yin maganar ba, har ma su furta cewa akwai matsala game da harkar kiwon lafiya, kuma akwai bukatar gyara.”

“Sai dai kurum su yi gum, ko kuma su yi karya, idan dai ba an samu wani akasi ba. Amma ita wannan uwargida @aishambuhari, ba za ta yi wannan ba.” Inji Abdullahi.

A cewar Aliyu Abdullahi, Mai girma Aisha Buhari za ta yi magana ko da za a caccaketa. “Ya fiye mata yin magana a soketa, a kan ta yi tsit lokacin da ta ke da damar magana.”

Abdullahi ya yabawa Aisha Muhammadu Buhari a kan namijin kokarinta da kiran ayi gaskiya.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel