Yadda na bar kiwon shanu na zama babban dan jarida - Umaru Sanda ya wallafa labarin shi mai ban sha'awa

Yadda na bar kiwon shanu na zama babban dan jarida - Umaru Sanda ya wallafa labarin shi mai ban sha'awa

- Fitaccen dan aikin jarida dake aiki da Citi rediyo, Umaru Sanda, ya wallafa labarin rayuwar da yayi a baya ta hanyar sanya hotuna a shafin sadarwa

- Fitaccen dan jaridar ya wallafa hotunan tare da rubutu da ya nuna yadda rayuwar shi ta fara

- Sanda ya bayyana cewa a baya yayi aikin kora shanu, inda a yanzu kuma ya zama fitacce a shafukan sadarwa

Fitaccen dan jarida na kasar Ghana wanda ke aiki da Citi rediyo, Umaru Sanda, ya wallafa wani rubutu a shafinsa na sadarwa dake nuni da yadda rayuwar shi ta fara.

Sakamakon fitowa daga gida da basu da hali sosai, rayuwarshi ta yarinta ta kasance cike da kalubale, Sanda ya sha wahala sosai, inda yayi ta kokari wajen karatunshi.

Yadda na bar kiwon shanu na zama babban dan jarida - Umaru Sanda ya wallafa labarin shi mai ban sha'awa
Yadda na bar kiwon shanu na zama babban dan jarida - Umaru Sanda ya wallafa labarin shi mai ban sha'awa
Asali: Facebook

Sai dai kuma, duk da wannan kalubale da ya samu na rayuwa, yayi kokari wajen ganin ya zama daya daga cikin manyan 'yan jarida a kasar Ghana da kowa yake son sauraronsu.

A wani rubutu da yayi a shafin sadarwa, dan jaridar, ya bayyanawa mabiyansa yadda rayuwarsa ta fara. Sanda ya bayyana cewa a baya sai da yayi aikin kora shanu domin ya samu ya rayu.

Ya ce:

"Wannan ita ce rayuwar dana fi tunawa a lokacin dana ke aiki a wani fanni daban, aikin kiwon shanu."

Sanda ya wallafa wani bidiyo tare da wani rubutu a shafin sadarwar.

Da yake sharhi akan labarin nashi, wani mai amfani da shafin Facebook da ya bayyana cewa sunyi aji daya da shi a makaranta, ya bayyana yadda a baya ba ya iya biyan kudin makaranta.

"Na fito gari daya da Umaru Sanda Amadu, mai suna Asutsuare, kai hatta makaranta ma daya muka yi, a lokacin yana ajin gaba dani, kuma zan iya gaya muku hatta a ranar da zamu rubuta jarrabawar gama firamare bashi da kudin da zai iya biya ya rubuta wannan jarrabawa, bayan malaman sun gane yadda yake da kokari a aji sai suka hada kudi suka je har daji suka dauko shi a gaban shanayen shi ya zo ya rubuta," ya ce.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel