NDLEA za ta fara gwajin kwaya na dole ga matan da ke shirin aure

NDLEA za ta fara gwajin kwaya na dole ga matan da ke shirin aure

Hukumar kula da fasa kwabrin miyagun kwayoyi (NDLEA), ta ce tana tunanin sakin sabuwar dokar da za ta tilasta yi wa 'yan mata gwajin miyagun kwayoyi kafin aurensu.

Shugaban hukumar, Mohammed Mustapha Abdalla, ya bayyana hakan ne yayin kona miyagun kwayoyin da suka kwace a Maiduguri, babban birnin jihar Borno a ranar Juma'a, 21 ga watan Augusta.

Kamar yadda Abdalla ya bayyana, akwai bukatar a fara gwajin miyagun kwayoyi a cikin jerin gwaje-gwajen da za a mika wa majami'u ko masallatai kafin daura aure.

An fara wannan tunanin ne sakamakon yadda 'yan mata da matan aure suka bayyana da ta'ammali da miyagun kwayoyi a fadin kasar nan.

Ya ce kiyasin cikin kwanakin nan ya nuna cewa, yawan masu ta'ammali da miyagun kwayoyi na raguwa a cikin maza amma yana karuwa a cikin mata matasa da matan aure.

"Domin fadada sabbin dokokin hukumar, NDLEA na tunanin fara hada kai da shugabannin addinai wurin mayar da gwajin miyagun kwayoyi ya zama dole cikin jerin gwaje-gwajen da za a mika sakamakonsu kafin daura aure.

"Bai kamata a halin yanzu mu ci gaba da nuna halin ko in kula ba a kan matsalolin da al'umma ke ciki ba. Alhakinmu ne shawo kan matsalar ta'ammali da miyagun kwayoyi.

“Gwamnatoci a kowanne mataki, yankuna da shugabannin addinai, iyaye, kafafen yada labarai, kungiyoyin matasa da masu tabbatar da dokoki, dole ne su dauki damarar yaki da miyagun kwayoyi," yace.

NDLEA za ta fara gwajin kwaya na dole ga matan da ke shirin aure
NDLEA za ta fara gwajin kwaya na dole ga matan da ke shirin aure. Hoto daga shafin Linda Ikeji
Asali: Twitter

KU KARANTA: Sanusi ya yi martani a kan janye gayyatar El-Rufai da NBA ta yi daga taronta

A wani labari na daban, a kalla 'yan bindiga 210 ne suka mika makamansu tare da sakin mutanen da suka yi garkuwa dasu a jihar Sokoto, in ji kwamishinan tsaro na jihar.

Col garba Moyi mai murabus, ya bayyana hakan a Sokoto yayin tofa albarkacin bakinsa akan makamai 102 da aka karba daga 'yan bindigar bayan sulhun da suka yi da gwamnatin jihar.

"Sun saki wadanda suka yi garkuwa dasu fiye da mutane 30 har da 'yan jihohin Zamfara da Kebbi. muna tattaunawa dasu na tsawon lokaci kuma munyi yarjejeniya dasu. Yarjejeniyar itace ta sakin wadanda suka sace," yace.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel