Kisan matar babban limami a Arewa: 'Yan sanda sun kama mutum 3 da ake zargi

Kisan matar babban limami a Arewa: 'Yan sanda sun kama mutum 3 da ake zargi

- Rundunar 'yan sandan jihar Kogi ta sanar da damke mutum 3 da take zargi da kashe matar babban limamin jihar

- Wani ganau ba jiyau ba, ya sanar da cewa 'yan ta'addan sun halaka Yemisi Baderu a gaban mijinta da 'ya'yanta

- Kakakin rundunar 'yan sandan jihar, DSP William Aya, ya tabbatar da aukuwar lamarin kuma ya ce ana bincikar wadanda ake tuhuma

A kalla mutum uku ne suka shiga hannun rundunar 'yan sandan jihar Kogi sakamakon zarginsu da ake da kashe matar babban limamin yankin Stereo, Yemisi Baderu, a karamar hukumar Ijumu ta jihar.

Wani ganau ba jiyau ba, ya ce an kashe matar a ranar Alhamis a cikin gidanta a kan idon mijinta da 'ya'yanta.

Jaridar The Punch ta ruwaito cewa, an halaka matar ne da adda.

Kakakin rundunar 'yan sandan jihar, DSP William Aya, yayin tabbatar da aukuwar lamarin, ya ce an kama wadanda ake zargin kuma ana tuhumarsu.

A wani bangare kuwa, babban mai bada shawara a kan harkar tsaro na yankin, Taufiq Isa, wanda ya ziyarci yankin a ranar Asabar, ya kwatanta lamarin da rashin imani.

Kisan matar babban limami a arewa: 'Yan sanda sun kama mutum 3 da ake zargi
Kisan matar babban limami a arewa: 'Yan sanda sun kama mutum 3 da ake zargi. Hoto daga The Punch
Asali: Twitter

KU KARANTA: Abubuwa 3 da suka kawo Muhammadu Sanusi II arewa

A wani labari na daban, rundunar 'yan sandan jihar Ribas ta bayyana sufeton ta da take zargin sojoji sun kashe da bugu a jihar.

Jami'in hulda da jama'a na hukumar 'yan sandan jihar, Nnamdi Omoni, ya bayyana jami'in dan sandan da suna Hosea Yakubu, inda ya kara da cewa har yanzu suna cigaba da bincike akan lamarin.

An gano cewa wasu sojoji dake gadin wani kamfani ne suka kashe wannan dan sanda bayan ya karya dokar bin hanya a gaban kamfanin a ranar Lahadi 16 ga watan Agusta, 2020.

Dan uwan wannan jami'in dan sanda da yayi hira da PUNCH akan wannan aika-aika ya bukaci a boye sunansa, inda ya ce: "Dan uwana tare da 'yan sanda guda biyu sun ki bin dokar hanya sakamakon shinge da aka sanya a gaban kamfanin na Eleme Petrochemical, sai wani soja ya tsare su, musu yayi nisa har ya zama fada.

"Daya daga cikin sojojin wanda ya shiga fadan yayi amfani da katon falanki ya makawa dan uwana a kai, take ya fadi ya daina motsi. Cikin gaggawa aka garzaya dashi asibiti don ceto rayuwar shi."

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel