2023: Dogara ya magantu a kan rade-radin takararsa

2023: Dogara ya magantu a kan rade-radin takararsa

Tsohon kakakin majalisar wakilai, Yakubu Dogara, ya musanta rade-radin da ke yawo na cewa yana hangen fitowa takarar mataimakin shugaban kasa a zaben 2023.

Kwanan nan Dogara ya bar jam'iyyar PDP inda ya koma APC, ya yi dogaro da rashin jituwa da kuma banbance-banbance da ke tsakaninsa da gwamnan jiharsa, Bala Mohammed na jihar Bauchi.

Tun daga nan, kafafen sada zumuntar zamani suke wallafa labaransa hadi da hotunansa, wandanda ke bayyana cewa zai fito takarar mataimakin shugaban kasa tare da shugaban APC, Bola Tinubu, wanda aka ce yana kokarin fitowa takarar shugabancin kasa.

Mai bada shawara ta musamman ga Dogara a kan kafafen yada labarai, Turaki Hassan, ya fitar da takarda a ranar Lahadi, inda yake cewa "akwai sauran shekaru kafin zuwan 2023. Don haka babu amfanin fara wasu hasashe. A maimakon hakan, zai fi idan aka hada karfi da karfe wurin shawo kan kalubalen da kasar nan ke fuskanta.

"Bugu da kari, a iya saninmu, babu jam'iyyar siyasar da ta fara siyar da fom na nuna bukatar takara.

"A don haka, za mu ce yayi wuri da wani ya fara ikirarin cewa wani zai tsaya takarar mataimakin shugaban kasa a lokacin da babu jam'iyyar da ta tsayar da dan takara," yace.

2023: Dogara ya magantu a kan rade-radin takararsa
2023: Dogara ya magantu a kan rade-radin takararsa. Hoto daga Daily Trust
Asali: UGC

KU KARANTA: Hotuna da bidiyon Sanusi II a ziyararsa ta farko a arewa bayan saukarsa sarauta

Idan za mu tuna, jam'iyyar PDP ta bayyana cewa, kokarin samun kujerar shugaban kasa ko mataimakin shugaban kasa ne yasa tsohon kakakin majalisar wakilai, Yakubu Dogara, ya koma jam'iyyar APC.

Shugaban kwamitin yardaddun jam'iyyar PDP, Sanata Walid Jubrin, ya bayyana hakan a wata takarda da ya fitar a Abuja a ranar Litinin, jaridar The Nation ta ruwaito.

A ranar Juma'a, shugaban kwamitin rikon kwarya na jam'iyyar APC, Alhaji Mai Mala Buni, ya sanar da sauya shekar Dogara zuwa jam'iyyar, jim kadan bayan ganawar tsohon kakakin majalisar da shugaban kasa Muhammadu Buhari a gidan gwamnati.

Dogara, wanda ya fito daga jihar Bauchi, ya danganta barin jam'iyyar PDP da yayi da banbancin da aka kasa sasantawa tsakaninsa da Gwamna Bala Mohammed na jihar.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
APC
Online view pixel