Tsohon na hannun daman shugaba Buhari ya bayyana dan yankin Kudu da zai gaji Buhari a 2023

Tsohon na hannun daman shugaba Buhari ya bayyana dan yankin Kudu da zai gaji Buhari a 2023

- An bukaci APC ta kyale Bola Ahmed Tinubu ya fito takarar shugaban kasa a 2023

- Tsohon sakataren gwamnatin tarayya Babachir Lawal shine ya bayyana haka a lokacin da yake magana akan siyasar 2023

- Lawal ya ce jigo a jam'iyyar APC din dan siyasa ne, kuma shine babban dalilin da ya sanya shugaba Buhari ya lashe zabe a 2015

Tsohon sakataren gwamnatin tarayya, Babachir Lawal, ya tasowa da tsohon gwamnan Legas Bola Ahmed Tinubu da zancen takarar shugaban kasa a shekarar 2023.

Lawal, wanda ya bayyana ra'ayinsa a zaben shekarar 2023, da kuma inda ya kamata su sami kujerar a wannan karon, ya ce dole a goyawa jigon jam'iyyar ta APC baya domin kuwa yayi rawar gani ga jam'iyya mai mulki.

Tsohon na hannun daman shugaba Buhari ya bayyana dan yankin Kudu da zai gaji Buhari a 2023
Tsohon na hannun daman shugaba Buhari ya bayyana dan yankin Kudu da zai gaji Buhari a 2023
Asali: UGC

A cewar shi, jigon na jam'iyyar APC shine babban dalilin da ya sanya tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan ya fadi zabe a shekarar 2015.

Da yake magana game da tsohon gwamnan Legas din, Lawal ya siffanta Tinubu a matsayin mutum mai hangen nesa, sannan kuma mutumin da shi kadai ya san lokacin da ya kamata ya dauki mataki akan abu.

KU KARANTA: Shugabannin kasuwa ne suke biyanmu mu fasa shagunan abokanan sana'arsu muyi musu sata - Cewar wasu barayi

"Tinubu baya son a yaba mishi akan abubuwan da yake; cikakken dan siyasa ne, yana samun kudin shi a siyasa, sannan ya rabar shi a siyasa. Bashi da wani buri da ya wuce siyasa.

"Kudin da ya kashe daga cikin aljihunsa ga jam'iyyya ba tare da sanin jam'iyya ba Allah yayi yawa da su. Na san da haka saboda shi abokina ne, kuma saboda nima ina daya daga cikin magoya bayan shugaba Buhari.

"Saboda haka, sai dai idan muna son fushin Allah a kanmu, inda na san ba abinda muke so ba kenan, dole jam'iyyar mu ta bawa kowa dama ga duk wanda yake bukatar fitowa takara, ciki kuwa hadda Tinubu, saboda haka mu taru mu zabi Bola," cewar tsohon sakataren gwamnatin tarayyar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel