Mace mai kamar maza: Ta yi watsi da daukar 'yan aiki ta zage dantse tana gina gidanta da kanta

Mace mai kamar maza: Ta yi watsi da daukar 'yan aiki ta zage dantse tana gina gidanta da kanta

- Wata mata mai suna Zamanzini Philisiwe Zungu, wacce ta karatu a fannin injiniya ta zage tana gina gidanta da kanta

- An dauki hoton Zungu tana jera bulo a gidan nata yayin da take kokarin cin karfin aikin nata

- Mutane da yawa sun yaba da wannan namijin kokari nata, inda suka yi mata addu'ar dacewa a shafukan sadarwa

Su waye suka ce mata baza su iya yin aikin da maza suke yi ba? Wata mata mai suna Zamazini Philisiwe Zungu, ta fito ta bayyanawa duniya cewa mata zasu iya maye gurbin maza a wuraren aiki.

Zungu dai tayi karatu a fannin injiyanci, inda ta yanke shawarar kara fadin gidanta, maimakon ta dauki 'yan aiki, matar ta tashi da kanta ta zage dantse tayi aikin da kanta.

Mace mai kamar maza: Ta yi watsi da daukar 'yan aiki ta zage dantse tana gina gidanta da kanta
Mace mai kamar maza: Ta yi watsi da daukar 'yan aiki ta zage dantse tana gina gidanta da kanta
Asali: Facebook

Ta wallafa hotonta a shafin Facebook a lokacin da take wannan aiki, inda tace:

"Wannan shine aikin dana fi iyawa."

Wata mata mai suna Nompilo Majozi, ta wallafa wannan hotuna na Zungu a shafinta na Facebook, inda ta ce:

"Idan har wannan bai burgeka ba, ban san mai zai burgeka ba. 'Yar uwa tayi karatun injiniyanci a jami'a, yanzu ga abinda take yi a gidanta. Sunanta Zamanzini Philisiwe Zungu...Ina matukar farin cikin kasancewata mace!"

KU KARANTA: Rashin hankaline ace daliban da suka gama jami'a da sakamako mai kyau suna neman aiki - Muhammad Akanbi

Mutane da dama sun yaba da wannan namijin kokari na Zungu, inda suka dinga tofa albarkacin bakinsu suna yaba mata.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel