Yadda jirginmu ya kusa ragargajewa a sararin samaniya - Aisha Buhari

Yadda jirginmu ya kusa ragargajewa a sararin samaniya - Aisha Buhari

Uwargidan shugaban kasar Najeriya, AIsha Muhammadu Buhari, ta bayyana abinda ta fuskanta yayin da take cikin jirgin dakarun sojin saman Najeriya (NAF), yayin da take dawowa daga UAE bayan duba lafiyarta da ta je yi.

A yayin sanar da dawowarta, matar shugaban kasan a wata takarda da ta fitar a ranar Asabar, ta bayyana yadda wata iska mai karfi a sararin samaniya ta kusa ragargaza jirgin da take ciki.

Ta bayyana kwarewa da dagewar matukin jirgin da zama daya daga cikin abinda ya tseratar da su.

Ta ce: "A yayin da muke kan hanyarmu ta dawowa, jirgin dakarun sojin saman Najeriya ya ci karo da wata iska, wacce kwarewa da jajircewar matukin jirgin da mukarrabansa yasa muka tsallaketa.

"Ina so in yi jinjina tare da mika godiya ta ga kwararren matukin jirgin da kuma tawagarsa, zakakuran sojin saman Najeriya maza da mata a kan kokarinsu da kuma masu kula da gyaran jiragen saman."

Yadda jirginmu ya kusa ragargajewa a sararin samaniya - Aisha Buhari
Yadda jirginmu ya kusa ragargajewa a sararin samaniya - Aisha Buhari. Hoto daga Aisha Buhari
Asali: Facebook

Uwargidan shugaban kasar ta mika godiyarta ga 'yan Najeriya da masoyanta a kan addu'o'insu. "Na dawo lafiya cike da koshin lafiya. Na dawo gida Najeriya bayan samun saki," tace.

Uwargidan shugaban kasa Muhammadu Buhari, ta kara da mika godiyarta ta musamman ga zakakuran masana kiwon lafiya na fadin kasar nan a kan yadda suke fuskantar yaki da muguwar annobar da ta zama ruwan dare.

KU KARANTA: Kano: Matashi ya sha alwashin kashe kansa ranar auren Hanan Buhari

A ranar 7 ga Agusta, mun kawo muku rahoton cewa an garzaya da uwargidan shugaba Muhammadu Buhari, Hajiya Aisha Buhari, birnin Dubai, kasar UAE don jinyar ciwon wuyan da take fama da shi tun bayan zuwanta Legas, Daily Trust ta ruwaito.

An samu labarin cewa uwargidan shugaba Muhammadu Buhari ta tafi Dubai ne tun washe garin Sallah sakamakon ciwon wuya da take fama dashi bayan komawa birnin tarayya Abuja daga jihar Legas.

Yayin da ta koma Abuja, ta killace kanta na tsawon makonni biyu saboda ciwon wuyan da take fama da shi na kimanin wata daya bayan ta'aziyyar.

Abin ya tayar da hankalin na kusa da uwargidan kuma hakan ya sa aka garzaya da ita birnin Dubai don ganin Likita.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel