Mamman Daura na cikin koshin lafiya - 'Dansa (Bidiyo)

Mamman Daura na cikin koshin lafiya - 'Dansa (Bidiyo)

- Wani sabon bidiyo ya bayyana a yanar gizo dake nuna ainihin halin da aminin Buhari, Mamman Daura ke ciki

- Daya daga cikin 'yayansa, Mohammed, ya bayyanawa duniya lafiyan ubansa kalau

- A bidiyon dai an ga Mamman Daura yana waya kuma da alamun lafiyansa kalau sabanin rahotannin kafafen sada zumunta

Wani faifan bidiyon aminin shugaba Muhammadu Buhari kuma dan'uwansa, Mamman Daura, mai nuna yana cikin koshin lafiya a kasar Birtaniya ya bayyana a kafafen sada zumunta.

An saki bidiyon ne domin karyata rahotannin dake yawo cewa aminin Buharin na gadon asibiti a kasar Ingila yana jinyan cutar Korona.

A bidiyon, dattijon mai shekaru 80 a duniya na tafiya yana waya cikin daki yana magana da harshen Hausa yana kyalkyacewa da dariya.

Mamman Daura na cikin koshin lafiya - 'Dansa (Bidiyo)
Mamman Daura na cikin koshin lafiya - 'Dansa (Bidiyo)
Asali: UGC

KU KARANTA: Kamar Jigawa da Bauchi, lauyoyin Yobe sun yi uwar kungiya bore saboda janye gayyatar El-Rufa'i

Daya daga cikin 'yayansa, Mohammed, ya yi karin haske kan lamarin inda yace Ubansa na cikin koshin lafiya.

Ya yiwa jaridar Thisday bayanin cewa mahaifinsa bai fama da wani matsalar numfashi ko ciwon koda.

"Tsawon yan kwanaki yanzu, an tilasta mana karyata rahotannin karya kan lafiyan mahaifinmu."

"Alhamdulillah. Baba na cikin koshin lafiya. Bai da matsalar koda ko wahalan numfashi kamar yadda yada radawa a labaran karya," Mohammed yace.

Wadanda ke murna kan labarin, ya ce "su sani cewa a rayuwan nan babu wanda zai dawwama. Saboda haka muyi kankan da kai saboda zamu mutu." Ya kara.

Kalli bidiyon:

A ranar 19 ga Agusta, rahoton Sahara Reporters ya bayyana cewa an fita da dan'uwan shugaba Muhammadu Buhari kuma amininsa, Alhaji Mamman Daura, kasar Birtaniya don ganin Likita bisa rashin lafiyan da yake fama.

A cewar rahoto, an fitar da Mamman Daura ne yau Laraba cikin jirgi bayan ya fara fama da matsalar numfashi da wasu alamomin kamuwa da cutar Korona tun ranar Juma'a.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel