Zaben Edo: DSS sun gayyaci shugabannin APC 10 zuwa muhimmin taro

Zaben Edo: DSS sun gayyaci shugabannin APC 10 zuwa muhimmin taro

Hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) ta gayyaci shugabannin jma'iyyar APC 10 a jihar Edo zuwa wani muhimmin taro a hedikwatarta ta jihar da ke birnin Benin.

DSS ta bukaci shugabannin jam'iyyar su halarci wani muhimmin taro da za a yi dasu a hedikwatarta ranar Asabar.

Wasikar, wacce gidan talabijin na Channels ya gani a ranar Juma'a, na dauke da kwanan watan 20 ga watan Agusta, wanda ya yi daidai da ranar Alhamis.

Duk da hukumar DSS ba ta bayyana abinda za ta tattauna da 'yan siyasar ba, ana zargin ba zai rasa alaka da zaben gwamnan jihar da za a yi a cikin watan Satumba mai zuwa ba.

Wani bangare na wasikar ya bayyana cewa; "an umarceni na gayyaceka (Adun) zuwa wurin wani muhimmin taro da da darektan hukumar DSS na jiha a ranar Asabar"

An bukaci Adun ya halarci taron tare da shugaban kungiyar direbobi (RTEAN) da sauran wasu shugabannin ja'iyyar APC 8.

Zaben Edo: DSS sun gayyaci shugabannin APC 10 zuwa muhimmin taro
Jami'an DSS
Asali: UGC

Shugabannin jam'iyyar 8 sune kamar haka; Ehis Adams (shugaban APC a Oredo), Osaro Idahosa (shugaban APC a Ikpoba-Okha), da Okunbor Roberts (shugaban APC a karamar hukumar Ovia ta kudu maso yamma).

Sauran sune; Atarodo (mamba a APC), Kingsley Amedo (mamba a APC), Richard Obe (mamba a APC), Osaro Idehen (mamba a APC) da Dakta Emma (mamba a APC).

DUBA WANNAN: Masaniyar zamantakewa ta bayyana dalilin yawaitar mutuwar aure a Najeriya

Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) ta tsayar da ranar 19 ga watan Satumba domin gudanar da zaben kujerar gwamnan jihar Edo.

Za a fafata a zaben a tsakanin gwamna mai ci, Godwin Obaseki, wanda ya fara lashe zaben kujerar gwamnan jihar Edo a shekarar 2016 a karkashin inuwar jam'iyyar APC, da abokin takararsa, Fasto Osagie Ize-Iyamu.

Ize-Iyamu ne ya sha kaye a hannun Obaseki a zaben shekarar 2016 lokacin da ya yi takarar neman kujerar gwamnan jihar Edo a karkashin inuwar jam'iyyar PDP.

Yanzu al'amura sun juya, Obaseki ya na takara a karskahin inuwar jam'iyyar PDP yayin da Ize-Iyamu ke takara a karkashin inuwar jam'iyyar APC.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel