Pantami ya shawarci matasa su rungumi wani abu guda da yafi karatun digiri muhimmanci

Pantami ya shawarci matasa su rungumi wani abu guda da yafi karatun digiri muhimmanci

Ministan harkokin sadarwa da gina tattalin arziki ta hanyar fasahar zamani, Dakta Isa Ali Pantami, ya jaddada bukatar 'yan Najeriya su bawa koyon sana'o'i muhimmanci fiye da karatun digiri.

A cewar ministan, yin hakan zai bawa 'yan kasa damar samun guraben da zasu taka muhimmiyar rawa wajen gina tattalin arzikinsu da na kasa baki daya.

Da ya ke magana a wurin wani taron tattaunawa da jama'a a Abuja, Pantami ya bayyana cewa yanzu duk kasashen da suka cigaba sun fi mayar da hankali a kan koyon sana'o'i da dabarun dogaro da kai.

A cewar Pantami, Najeriya ba zata samu wani cigaba na kirki ba matukar ba ta bayar da fifiko ga koyar da matasa sana'o'i da dabarun dogaro da kai ba.

Ministan ya bayar da misalin yadda kasar China ta mayar da jami'o'i 600 cibiyoyin koyar da sana'o'i a yayin da har yanzu Najeriya ke gina sabbin jami'o'i.

Dakta Pantami ya kara da cewa saboda muhimmanci da aka dorawa takardar sakamakon karatun jami'a, dalibai na rige-rige da gasar samun sakamakon karatu mai kyau.

Pantami ya shawarci matasa su rungumi wani abu guda da yafi karatun digiri muhimmanci
Dakta Pantami
Asali: UGC

Ya kara da cewa matukar Najeriya tana son cigaba, akwai bukatar ta sauya tsari tare da yin tambayar; "wacce jami'a Bill Gates ya halarta kuma da wanne irin sakamako ya fita da shi?

DUBA WANNAN: Ta'addanci: Mamba a majalissar dokokin jihar Benuwe ya samu matsuguni a kurkuku

A cewarsa, a kasashen duniya da dama ba a la'akari da zurfin karatu ko tarin takardun kammala makaranta da mutum ya mallaka kafin a dama da shi a wasu harkoki, ana damawa da mutum ne saboda irin dabarun da yake dasu.

Ya bayyana cewa lokaci ya yi da ya kamata Najeriya ta fara koyi da sauran kasashen da suka cigaba, inda ba a bukatar takardar kammala wata makaranta kafin a bawa mutum aiki.

Ministan ya kara da cewa akwai mutane da yawa da ke taka rawar gani a bangaren fasahar sarrafa bayanai (ICT) duk da basu da takardar shaidar kammala wani karatu mai nasaba da ICT.

(NAN)

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel