Tawagar UN ta ziyarci hamɓararren Shugaban Mali, Boubacar Keita

Tawagar UN ta ziyarci hamɓararren Shugaban Mali, Boubacar Keita

Majalisar Dinkin Duniya a ranar Juma'a ta ce ta samu ganin hambararren Shugaban kasar Mali a yayin da masu tayar da kayan bayan suka ce sun sako mutum biyu cikin shugabannin da suka tsare bayan kasashen duniya sun matsa musu lamba.

"A daren jiya, wata tawaga daga MINUSMA, kungiyar kare hakkin bil adama ta tafi Kati a yunkurin aikinta na kare hakokin yan adam kuma ta samu ganin Shugaba Ibrahim Boubacar Keita da wasu da aka tsare," a cewar tawagar samar da zaman lafiya ta UN.

Kati sansanin sojoji ne da ke kusa da babban birnin kasar, Bamako inda ake tsare da wadanda aka kama yayin juyin mulkin da aka yi a ranar Talata a kasar ta Mali da aka dade ana rikici.

Kazalika, wani majiya da ya nemi a boye sunansa ta ce ta bawa "tawagar UN" izinin zuwa su gana da dukkan fursunonin 19 da ke tsare a Kati ciki har da Keita da Farai minista, Boubou Cisse.

Tawagar UN ta ziyarci hambararren Shugaban Mali, Boubacar Keita
Tawagar UN ta ziyarci hambararren Shugaban Mali, Boubacar Keita. Hoto daga The Punch
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Yadda wata budurwa ta yi garkuwa da kanta domin samun kuɗi daga iyayenta

Majiyar ta ce masu juyin mulkin sun saki tsohon ministan tattalin arzikin kasar Abdoulaye Daffe da Sabane Mahalmoudou, sakataren shugaba Keita.

"An sako fursunoni biyu. Har yanzu akwai 17 da suka yi saura a Kati. Wannan alama ce da ke nuna muna mutunta hakkokin yan adam," a cewar daya daga cikin jamian gwamnatin sojin.

Sojoji masu tayar da kayar baya sun kama Keita da wasu shugabannin gwamnati bayan sun yi juyin mulki a Kati, wani sansani da ke nisan kilomita 15 daga babban birnin kasar wato Bamako.

Sun saka wa kungiyarsu suna Kwamitin Kasa na Ceto Alumma, karkashin jagorancin Kwanel Assimi Goita kuma sun sha alwashin za su gudanar da zabe a lokacin da ya dace.

Kungiyoyin ECOWAS, AU, EU, Amurka da Majalisar Tsaro ta Majalisar Dinkin Duniya duk sunyi Allah wadai da juyin mulkin kuma sun bukaci a sako Keita da sauran shugabannin gwamnatin da aka tsare.

Wannan juyin mulkin shine na biyu cikin shekaru 8 a Mali, kuma hakan zai yi wa kasar illa sosai duba da cewa ta dade tana fama da yan taadda, tabarbarewar tattalin arziki da kiyayya da mutane ke yi wa gwamnati.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel