Mun samu labarin cafke Harry Maguire a Mykonos – Manchester United

Mun samu labarin cafke Harry Maguire a Mykonos – Manchester United

Harry Maguire ya fada hannun hukuma a birnin Mykonos, a kasar Girka. Mun samu wannan labari ne daga Skysports a ranar Alhamis, 20 ga watan Agusta.

Bayan sa’o’i da aukuwar wannan lamari, Kungiyar Manchester United ta tabbatar da cewa ta samu labarin tsare ‘dan wasan bayan na ta mai shekaru 27.

Ga jawabin da kungiyar Manchester ta fitar dazu, “Kulob dinnan ya samu labarin rikicin da Harry Maguire ya shiga a garin Mykonos a daren jiya.”

“Mun tuntubi Harry Maguire, kuma ya na ba jami’an tsaron kasar Girka hadin kai.”

Yayin da ake cigaba da bincike, Manchester United ba ta ce uffan ba bayan wannan jawabi da ta yi. “A wannan gaba, ba za mu sake cewa komai ba.”

Goal.com ta fitar da rahoto cewa an kama ‘dan wasan ne da laifin fada da cin mutuncin ‘yan sanda da fatar baki. Hakan ya faru ne a Mykonos, wani tsibiri a Girka.

KU KARANTA: Buhari ya naɗa Amokaci a matsayin mai bada shawara

Mun samu labarin cafke Harry Maguire a Mykonos – Manchester United
Harry Maguire ya shiga matsala Hoto: LFC
Asali: Getty Images

‘Dan wasan bayan wanda yanzu ya ke hutawa tare da iyalinsa bayan an kammala kakar wasannin bana ya zagi jami’in tsaro ne a jiya.

Wani kakakin ‘yan sanda, Petros Vassilakis, ya shaidawa ‘yan jarida cewa sabani ya shiga tsakanin tawagar ‘dan wasan Manchester United da wasu Bayin Allah.

“Bayan an sasanata rigimar, sai bangaren ‘dan wasan su ka rika zagin jami’an ‘yan sanda.”

Vassilakis ya ce “Akwai ‘yan sanda rututu a wurin. Bayan wani lokaci sai daya daga cikin mutane uku da ke cikin tawagar ya jefi ‘yan sanda, daga nan fada ya kaure.”

Yanzu duka wadannan mutane uku; har da ‘dan wasan Man Utd su na tsare. An bada shekarun sauran wadanda aka kama da 28 da 29.

“Za su bayyana a gaban kuliya a tsibirin Syros an jima bisa laifin kai wa ‘yan sanda hari.”

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng