Mutum uku sun rasa rayukansu, yayin da aka kone gidaje masu yawan gaske a wani sabon rikici da ya barke tsakanin kabilar Tiv da Jukun

Mutum uku sun rasa rayukansu, yayin da aka kone gidaje masu yawan gaske a wani sabon rikici da ya barke tsakanin kabilar Tiv da Jukun

Wani sabon rikici da ya barke tsakanin kabilar Tiv da Jukun yayi sanadiyyar mutuwar mutane uku, inda kuma aka kone gidaje masu yawan gaske a kauyen Dananacha dake karamar hukumar Gassol cikin jihar Taraba

Mutane uku sun mutu sannan kuma an kone gidaje masu yawan gaske sakamakon sabon rikici da ya barke tsakanin kabilar Tiv da Jukun a garin Dananacha, dake cikin karamar hukumar Gassol, cikin jihar Taraba.

Daily Trust ta ruwaito cewa rikicin ya samo asali ne bayan rikici da ya barke tsakanin matasan kabilar Tiv da Jukun a garin ranar Laraba.

Mutum uku sun rasa rayukansu, yayin da aka kone gidaje masu yawan gaske a wani sabon rikici da ya barke tsakanin kabilar Tiv da Jukun
Mutum uku sun rasa rayukansu, yayin da aka kone gidaje masu yawan gaske a wani sabon rikici da ya barke tsakanin kabilar Tiv da Jukun
Asali: Original

Daga baya kuma an sake ruwaitowa cewa dattijan kabilun guda biyu sun daidaita tsakanin matasan, amma ranar Alhamis da safe, rikicin ya kara barkewa tsakanin matasan.

Garin na Dananacha nata fuskantar rikici tsakanin kabilun guda biyu shekaru da dama, inda hakan yayi sanadiyyar kashe daruruwan mutane da kuma bata dukiyoyi masu yawan gaske.

Yanzu haka dai garin an raba shi gida uku; inda bangare daya kabilar Jukun suke zaune, sauran bangare guda biyun kuma kabilar Tiv da Hausa-Fulani ke zaune.

KU KARANTA: An kama likitan bogi da yake bawa mutane maganin coronavirus a Najeriya

Wani wanda lamarin ya faru kan idonsa mai suna Musa Rabiu, ya bayyanawa wakilin Daily Trust cewa rikicin ya samo asali ne sakamakon kokari da kabilun suke na canjawa garin suna daga Dananacha zuwa Kwararafa, inda hakan ya jawo rikici tsakaninsu.

Rabiu ya cigaba da cewa wannan rikici ya jawo rudani sosai a yankin inda mutane da yawa da suka hada da mata da yara suke guduwa daga garin.

Kabilun guda biyu dai an ruwaito cewa sun tada matasa da suke kaiwa juna hari a gidajensu, duk kuwa da cewa an hana duka kabilun daukar makamai don yakar juna.

Da aka tuntubi kakakin rundunar 'yan sandan jihar, David Misa, ya ce a jiya kabilar Tiv da Jukun sun samu hatsaniya, amma babu wanda ya mutu.

Ya ce 'yan sanda sun shiga tsakani kuma komai ya daidaita.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel