Yan sanda sun ceto mutumin da aka rufe shi a gida tsawon shekaru 15 a Sokoto ba fita

Yan sanda sun ceto mutumin da aka rufe shi a gida tsawon shekaru 15 a Sokoto ba fita

Ƴan sanda jihar Sokoto sun ceto wani mutum mai shekaru 45, Salisu Muhammad da kawunsa ya ɗaure shi a gida na tsawon shekaru 15 a Gidan Madi a ƙaramar hukumar Tangaza.

An ce Muhammad wadda ke da yarinya da ta girma yana fama da taɓin hankali ne kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Hajiya Ubaida Bello, mai bawa Gwamna Aminu Tambuwal shawara a kan Hakokin Bil Adama da Kungiyoyin tallafawa al'umma ce makwabta ne suka sanar da hukuma game da halin da ya ke ciki don da farko sunyi tsammanin ya mutu ne.

Yan sanda sun ceto mutumin da ake rufe shi na shekaru 15 a Sokoto
Yan sanda sun ceto mutumin da ake rufe shi na shekaru 15 a Sokoto
Asali: Depositphotos

"Da farko sunyi tsammanin ya mutu ne domin ba su gan shi ba a waje na tsawon shekaru fiye da goma.

"Da suka gano halin da ya ke ciki, sun sanar da mu cikin gaggawa.

"Daga nan ne muka tattara ƴan sanda, masu kare hakkin bil adama da wasu ma'aikatan ƙaramar hukuma ciki har da shugaban ƙaramar hukuma muka tafi gidan muka ceto shi," in ji ta.

An gano wasu mata biyu a gidan ciki har da ƴarsa mai shekaru 19 wadda a yanzu ba ta san tsawon lokacin da ya yi a daure ba.

"Mun tarar da shi a cikin mummunan yanayi, yana bayan gida da fitsari a wuri guda ba tare da wani kulawa ba.

"Ya kasa yin tafiya da kansa ma saboda rashin samun abinci.

"Idan suna iƙirarin cewa yana fama da taɓin hankali ne me yasa ba su kai shi asibitin ƙwaƙwalwa ba domin ayi masa magani," in ji ta.

DUBA WANNAN: Yadda wata budurwa ta yi garkuwa da kanta domin samun kuɗi daga iyayenta

Wata majiya ta shaidawa Daily Trust cewa kawun mutumin ne da ke zaune a wani ƙauye nan kusa ya rufe shi.

Bello ta ce an garzaya da mutum asibitin ƙwaƙwalwa a karamar hukumar Ƙware yayin da ƴan sanda na cigaba da bincike don gano dalilin rufe shi.

Kakakin ƴan sandan jihar Sokoto ASP Muhammad Sadiq ya tabbatar da afkuwar lamarin inda ya ce binciken da suka fara yi ya nuna mutumin na da taɓin hankali.

"Kawo yanzu babu wanda aka kama a kan lamarin," in ji shi.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel