Faɗa ta kaure tsakanin magoya bayan APC da ADC a Ondo, an raunata mutane da dama

Faɗa ta kaure tsakanin magoya bayan APC da ADC a Ondo, an raunata mutane da dama

Ƙazamin rikici ya ɓarke tsakanin tsakanin magoya bayan jam'iyyar All Progressives Congress, APC da na African Democratic Congress, ADC, a garin Yaba da ke jihar Ondo.

The Punch ta ruwaito cewa mutane da dama sun samu raunuka kuma an lalata a ƙalla ababen hawa 15 a fadar da ta fara a yammacin ranar Alhamis.

Rikicin ya barke ne sa'o'i kadan kafin a fara zabukkan kananan hukumomi a jihar.

Faɗa ta kaure tsakanin magoya bayan APC da ADC a Ondo, an raunata mutane da dama
Faɗa ta kaure tsakanin magoya bayan APC da ADC a Ondo, an raunata mutane da dama. Hoto daga The Punch
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Za a yi wa matar da ta kashe dan ta a Kano gwajin kwakwalwa

A halin yanzu dai ba a tabbatar da dalilin da ya janyo rikicin ba a lokacin haɗa wannan rahoton amma an gano cewa rikicin ba zai rasa nasaba da zaɓen kananan hukumomi da za ayi a ranar Asabar mai zuwa ba.

Ku saurari ƙarin bayani...

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel