An kama likitan bogi da yake bawa mutane maganin coronavirus a Najeriya

An kama likitan bogi da yake bawa mutane maganin coronavirus a Najeriya

- 'Yan sanda sun cafke wani tsoho mai shekara 60 a duniya da laifin bayar da magunguna na bogi

- An kama shi yana bawa mutane maganin cutar coronavirus a babban birnin tarayya Abuja

Wani mutumi dan shekara 60 a duniya mai suna Charles George ya shiga hannun jami'an tsaron bayan kama shi yana bawa mutane maganin COVID-19.

Kungiyar kwararrun likitoci ta Najeriya, su suka tabbatar da kama mutumin a ranar Alhamis 20 ga watan Agusta, inda suka bayyana cewa an kama shi a wani gidansa mai daki daya, kwatas din ma'aikatan Julius Berger da aka fi sani da Berger Camp dake Kubwa, babban birnin tarayya Abuja.

An samu allurai da abubuwan zubar da ciki da sauransu a wajen shi, inda ake zargin yana yiwa mutane magani na bogi da ka iya jawo su dinga mutuwa babu gaira babu dalili.

An kama likitan bogi da yake bawa mutane maganin coronavirus a Najeriya
An kama likitan bogi da yake bawa mutane maganin coronavirus a Najeriya
Source: Depositphotos

'Yan sandan sun nuna wata takarda ta bogi da mutumin ya buga da kuma sakonni na waya da yake aikawa mutanen da yake so ya zalunta, kamar yadda sanarwar ta nuna.

"An kama George da laifin yin amfani da magunguna na bogi wajen tatsar kudi a wajen mutane, inda muka gurfanar da shi a ofishin mu dake Kubwa, akan laifuka da dama tun daga shekarar 2016."

KU KARANTA: Karti 30 sun yiwa yarinya 'yar shekara 16 fyade da karfin tsiya a wani otel bayan ta kwankwadi barasa

A nashi bangaren mataimakin rijistara na ofishin hukumar 'yan sandan Dr. Victor Gbenro ya ce:

"Wannan mai laifin ana zargin shi da bayar da magani ba tare da rijista ko samun lasisi ba, wanda yake tilas ne ga wadanda zasu yi aiki ko sana'a a wannan fannin su mallaki wannan takardu a Najeriya.

"Bincike ya nuna cewa abinda yake yi babu shi kwata-kwata a fannin lafiya ta kasa baki daya. 'Yan sanda kuma na cigaba da bincike akan mai laifin. Wannan yana daya daga cikin yunkurin da hukumar take yi wajen tsaftace fannin lafiya a kasar."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel