Buruji Kashamu ya janye kararsa da Adebutu kafin ya mutu inji Lauyansa

Buruji Kashamu ya janye kararsa da Adebutu kafin ya mutu inji Lauyansa

- Sanata Buruji Kashamu bai cika ba sai da ya yi sulhu da Keshington Adebutu

- Marigayin ya nemi afuwar Adebutu a lokacin da ya tabbatar ba zai iya tashi ba

- Lauyan Kashamu ya ce sun janye karar da su ka shigar kan kamfanin Adebutu

Lauyan da ya tsayawa Sanata Buruji Kashamu, Ajibola Oluyede, ya ce Marigayin ya janye karar da ya shigar a kan manyan kamfanoni har da na Keshington Adebutu.

Keshington Adebutu wanda aka fi sani da Baba Ijebu, shahararren Attajiri ne a Kudancin Najeriya wanda su ka yi ta samun matsala da Buruji Kashamu a lokacin ya na raye.

Lauyan Marigayin ya ce Kashamu bai bar Duniya ba sai da ya janye karar da kamfaninsa na Western Lotto Limited ya shigar kan kamfanin takwaransa Baba Ijebu.

Ajibola Oluyede ya shaidawa jaridar Punch wannan ne a wata hira da su ka yi ta wayar salula. Lauyan ya ce an janye wannan kara daga kotu ne kafin Kashamu ya cika.

KU KARANTA: Dai-bayan-daya: Daga Kyari, Funtua, ga Maida, na-kusa da Buhari su na ta tafiya

Buruji Kashamu ya janye kararsa da Adebutu kafin ya mutu inji Lauyansa
Sanata Buruji Kashamu
Asali: Depositphotos

An tuntubi wannan Lauya ne bayan wani bidiyo ya fito inda aka ji muryar Marigayi Sanata Kashamu ya na waya da Adebutu, ya na rokon Attajirin ya yafe masa.

Adebutu ya bukaci Buruji Kashamu ya janye karar da ya shigar a babban kotun tarayya da ke Legas a matsayin sharadin sulhu da jigon na jam’iyyar PDP mai hamayya.

Daga gadon asibiti, Kashamu ya fadawa Adebutu cewa sabani ne su ka rika samu da rashin fahimta, Sanatan ya bayyanawa ‘Dan kasuwar cewa ba fada ya ke yi da shi ba.

Oluyede wanda ya kasance ya tsayawa Kashamu a kotu, ya tabbatar da cewa sun janye kararsu a watan Agusta mai-ci. ‘Dan siyasar ya mutu da farin cikin ya yi sulhu da ‘dan garinsa.

Kashamu ya na cikin wadanda COVID-19 ta harba, a dalilin haka ne kuma ya rasu a wani babban asibiti da ke Legas. An bizne Marigayin ne a garin Ijebu-Igbo, jihar Ogun.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng