Kungiyar CAN ba ta goyon bayan dokar CAMA, ta kira sabuwar dokar ‘bam’

Kungiyar CAN ba ta goyon bayan dokar CAMA, ta kira sabuwar dokar ‘bam’

Kungiyar CAN ta kiristocin Najeriya ba ta goyon bayan dokar kamfanoni ta shekara 2020, ta ce dokar za ta hana coci sakat, kuma ta maida su karkashin gwamnati.

A cikin watan Agustan nan ne shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ratttaba hannu a kan dokar da aka kira CAMA, wanda wannan ta shafe tsohuwar dokar shekarar 1990.

Kiristocin Najeriya da ke karkashin CAN sun bayyana bangare na 839 na wannan doka da shaidanin sashe wanda ya ba Minista damar dakatar da shugabannin coci

Kafin yanzu mun samu wani bidiyo inda aka ji shararren faston nan, Bishof David Oyedepo, ya na jan-kunnen gwamnatin tarayya game da wannan doka da ta shigo da shi.

Wannan doka da ake a surutu a kai ta ba Ministan tarayya ikon korar shugabannin da ke kula da kungiya ko wani coci, ya nada wasu sababbi na rikon kwarya idan ta kama.

A wani jawabi da shugaban CAN na kasa, Dr. Samson Ayokunle ya fitar a ranar Alhamis, 20 ga watan Agusta, 2020, ya ce ba su goyon bayan wannan doka ka-co-kam.

KU KARANTA: Mai dakin Mulhidin da ya zagi addini ta fito ta na kuka

Kungiyar CAN ba ta goyon bayan dokar CAMA, ta kira sabuwar dokar ‘bam’
Kungiyar CAN tare da Shugaba Buhari
Asali: UGC

Wannan jawabi ya fito ne ta bakin wani Hadimin jagoran kiristocin kasar wanda ke taimaka masa wajen harkar yada labarai da sadarwa, Mista Adebayo Oladeji, ya ce:

“Wannan doka akalla ace ba za ta samu karbuwa ba, ta sabawa Ubangiji, abin tir ce kuma wanda ba ta da wani alheri tattare da ita. Bam ce da aka dasa, ana jiran ta tashi."

Ayokunle ya ke cewa: “Yayin da ba mu adawa da kokarin gwamnati na yaki da rashin gaskiya a duk inda ake same ta, amma ba mu goyon bayan a sa coci cikin rukunin NGOs.”

“Coci ba zai zama karkashin gwamnati ba domin nauyi da hakkokin da ke kansa.” Ya kuma ce, “Ta ya gwamnati za ta kori shugabannin cocin ba ta bada gudumuwar sisi wajen ginawa ba?”

Rabaren din ya ce bai kamata ‘dan siyasan da bai san harkar addini ba, ya sa baki a sha'anin coci. Ana iya ma samun wanda ba kirista ba ya zama Minista da zai sa wa coci ido.

CAN ta ce: “Idan gwamnati ta dage sai ta kawo wannan doka da duka kiristoci ba su goyon bayanta, to sun kira yaki ne da kiristanci, kuma su na kokarin rusa coci.”

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel